Gwamnatin tarayya ta ciyo bashin ton 5,000 na hatsi don ciyar da 'yan Nigeria

Gwamnatin tarayya ta ciyo bashin ton 5,000 na hatsi don ciyar da 'yan Nigeria

- Gwamnatin tarayya ta ce ta ciyo bashin ton 5,000 na hatsi daga rumbun ajiyar abinci na kungiyar ECOWAS

- Shuwagabannin kasashen ECOWAS sun yanke shawarar samar da shirin adana abinci don yaki da yunwa a kasashensu

- Gwamnati ta ce zai zama abu mai muhimmanci a taimaki marasa karfi musamman wadanda annobar COVID-19 ta shafa a Nigeria

Gwamnatin tarayya ta ce ta ciyo bashin ton 5,000 na hatsi daga rumbun ajiyar abinci na kungiyar hadakar kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS).

Ministan cikin gida kan noma da bunkasa karkara, Mustapha Baba-Shehuri, ya bayyana hakan yayin da yake karbar ton 3,999 daga ECOWAS a matsayin tallafi ga gwamnatin tarayya.

Ministan ya karbi ton 3,999 na hatsi a madadin gwamnatin tarayya a rumbun hatsi na Hotoro da ke jihar Kano, a cewar wata sanarwa a Abuja daga ma'aikatarsa.

Baba-Shehuri ya bayyana cewa shuwagabannin kasashen ECOWAS sun yanke shawarar samar da shirin adana abinci don yaki da yunwa a kasashensu musamman a kasashen hamada.

KARANTA WANNAN: Musa Mai Sana'a: Ina nadamar tsinewa kaina a fina-finan da na yi a baya

Gwamnatin tarayya ta ciyo bashin ton 5,000 na hatsi don ciyar da 'yan Nigeria
Gwamnatin tarayya ta ciyo bashin ton 5,000 na hatsi don ciyar da 'yan Nigeria
Asali: Depositphotos

Ya ce hakan ya tilasta kulla yarjejeniya tsakanin ECOWAS da sashen abinci da ajiyarsa na ma'aikatar noman a ranar 7 ga watan Yulin 2017.

Ministan yace, "Gwamnatin Nigeria ta ciyo bashin ton 5,000 na hatsi daga rumbun ajiyar hatsi na ECOWAS, bisa tsarin biyan bashin ta hanyar mayar da wani hatsin.

"Tuni aka gama shirin mayar da bashin kafin zuwan annobar COVID-19. Amma duk da haka, ina baku tabbacin cewar za a mayar da hatsin nan ba da jimawa ba."

Dangane da tallafin da ECOWAS ta bayar, ministan ya ce zai zama abu mai muhimmanci a taimaki marasa karfi musamman wadanda annobar COVID-19 ta shafa a Nigeria.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel