Dalilin da ya sa Bayern Munich ta lallasa PSG har ta dauki kofin UEFA 2020 - Hansi Flick

Dalilin da ya sa Bayern Munich ta lallasa PSG har ta dauki kofin UEFA 2020 - Hansi Flick

- Babban kocin Bayern Munich Hansi Flick ya bayyana dalilin da yasa kungiyar sa ta samu nasarar daukar kofin UEFA 2020

- Yan wasan sun nuna farin cikinsu ta hanyar cilla Flick a sararin samaniya suna cabewa bayan daga kofin, bayan lallasa PSG 1-0

- Keftin din Bayern, Neuer, daya daga cikin 'yan wasan da suka dade tun daga 2013, ya yi farin ciki na daga wannan kofi

Babban kocin Bayern Munich Hansi Flick ya nuna tsantsar murnarsa kan nasarar da kungiyar kwallonsa ta samu a watanni 9 tun bayan da ya fara horas da 'yan wasan kungiyar.

Murnar ta sa na zuwa ne bayan da Bayern Munich ta samu nasarar lashe kofin zakarun nahiyar turai a ranar Lahadi.

A karo na shida, Beyern ta lashe kofin UEFA, bayan da ta lallasa abokiyar karawarta, Paris Saint-Germain (PSG), da ci 1 mai ban haushi.

Yan wasan sun nuna farin cikinsu ta hanyar cilla Flick a sararin samaniya suna cabewa bayan daga kofin, cin da dan wasa Kingsley Coman ya yi da kai, a zagayen wasa na biyu.

A daya hannun kuwa, mai tsaron ragar Munich, Manuel Neuer, ya hana 'yan wasan PSG, Neymar da Kylian Mbappe zura kwallo a ragarsa duk da hare haren da suka kai masa.

KARANTA WANNAN: Tattalin arzikin Nigeria ya karye

Dalilin da ya sa Bayern Munich ta lallasa PSG har ta dauki kofin UEFA 2020 - Hansi Flick
Dalilin da ya sa Bayern Munich ta lallasa PSG har ta dauki kofin UEFA 2020 - Hansi Flick
Asali: Twitter

"Ina alfahari da kungiya ta. A lokacin da naga kanun labaran Nuwanba, kawai abunda na karanta shine babu sauran mai tsoron Bayern," cewar Flick, wanda ya maye gurbin Kovac.

"Amma tun daga zuwana kungiyar, aka ci gaba da samun canji mai amfani. Mun cancanci muyi nasara, saboda wasan da muka buga bayan dawowa daga hutun tsakiyar wasa.

"Za ku iya gasgatani, tun daga wasannin motsa jiki da muka rinka yi a watan Janairu, tun a lokacin 'yan wasan ke da yakinin samun nasara."

Wannan shine aikin Flick na farko a Germany, amma a kakar wasan farko ya kai ga nasara a Bayern, na samun kofin Bundesliga, kofin Jamus, ga kuma yanzu kofin UEFA.

Ya bi sahun tsohon kocin Bayern, Jupp Heynckes wanda ya kafa tarihi a kungiyar, musamman a shekarar 2013.

Bayan zama mataimakin koci ga Joachim Loew a lokacin da Germany ta lashe kofin duniya na shekarar 2014, Flick yanzu ya zama abun kwatance a kasar, sakamakon nasarar Bayern.

"Naji bakin ciki da babu masoyanmu a nan, amma da sa ran zasu biyo mu nan gaba, amma wasa irin wannan babu masoya ba wasan da muka saba gani bane," cewar Flick.

Keftin din Bayern, Neuer, daya daga cikin 'yan wasan da suka dade tun daga 2013, ya yi farin ciki na daga wannan kofi.

"Farin cikin na da yawa, abunda muka cancanci samu kenan, munyi fatan hakan, gashi mun samu, amma munyi aiki tukuru," cewar mai tsaron ragar kungiyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel