Da duminsa: Tattalin arzikin Nigeria ya karye

Da duminsa: Tattalin arzikin Nigeria ya karye

- NBS ta fitar da rahoto a ranar Litinin da ke nuni da cewa tattalin arzikin Nigeria ya karye da kashi –6.10

- A watan Maris ne Nigeria ta sanar da rufe iyakokin kasar a yunkurinta na dakile yaduwar cutar ta COVID-19 a fadin kasar

- Karyewar tattalin arzikin ya zo ne bayan shekaru uku na karancin tattali amma dai wanda ba za ace ya karye ba, tun bayan karyewarsa a 2016

Rahoton hukumar kididdiga ta kasa (NBS) a ranar Litinin na nuni da cewa tattalin arzikin Nigeria na cikin gida (GDP) ya karye da kashi –6.10.

Rahoton kididdigar GDP na watanni shida na shekarar 2020 ya nuna cewa tattalin arzikin ya karye ne saboda matsalolin tattalin arziki na cikin gida da wajen kasar da aka samu.

Sai dai rahoton ya yi nuni da cewa an fi samun koma baya daga watan Afrelu zuwa Yulin 2020.

Kasashen duniya sun kulle duk wata kafar tattalin arziki sakamakon barkewar annobar COVID-19.

A watan Maris ne Nigeria ta sanar da rufe iyakokin kasar a yunkurinta na dakile yaduwar cutar ta COVID-19 a fadin kasar.

KARANTA WANNAN: Shugaban kasar Brazil ya yi barazanar dukan dan jarida

Da duminsa: Tattalin arzikin Nigeria ya karye
Da duminsa: Tattalin arzikin Nigeria ya karye
Asali: Twitter

Hukumar NBS a ranar Litinin ta yi nuni da cewa dalilan karyewar tattalin arzikin kasar sun hada da sanya dokar ta baci ga mutane da ababen hawa a jihohin kasar.

Sauran sun hada da haramta tafiye tafiye ta jiragen sama, rufe makarantu da kasuwanni da dai sauran, wanda ya shafi kasuwancin cikin gida dana waje.

Wannan hukunci da gwamatin tarayya da na jihohi suka dauka, ya kawo koma baya sosai a watanni shidan farko na shekarar, kuma da yiyuwar ya wuce hakan.

Karyewar tattalin arzikin ya zo ne bayan shekaru uku na karancin tattali amma dai wanda ba za ace ya karye ba, tun bayan karyewarsa a 2016.

Cikakken rahoton yana zuwa...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel