Babbar magana: Shugaban kasa ya yi barazanar dukan dan jarida

Babbar magana: Shugaban kasa ya yi barazanar dukan dan jarida

- Shugaban kasar Brazil, Jair Bolsonaro a ranar Lahadi ya yi barazanar yiwa wani dan jarida mahangulba a baki

- Dan jaridar O Globo ya tambayi shugaban kasar akan gaskiyar rahoton jaridar Crusoe da ke alakanta uwar gidansa Michelle Bolsonaro da zargin rashawa

- Shugaban kasar ya yi watsi da zanga zanga daga sauran 'yan jarida bayan wancan furuci da yayi, ya kuma bar wajen ba tare da kara cewa komai ba

Shugaban kasar Brazil, Jair Bolsonaro a ranar Lahadi ya yi barazanar yiwa wani dan jarida mahangulba a baki.

Dan jarida, kamar yadda rahotanni suka bayyana, ya matsawa shugaban kasar da tambaya kan alakanta matarsa da wani zargin cin hanci da rashawa.

"Ina ji kamar na yi maka mahangulba a baki," shugaban kasar ya sanarwa dan jaridar daga kamfanin jarida na O Globo, bayan tambayarsa.

Dan jaridar na daga cikin tawagar da ta gana da Bolsonaro bayan ziyarar ranar Lahadi da ya saba kaiwa cocin Cathedral of Brasília.

Shugaban kasar ya yi watsi da zanga zanga daga sauran 'yan jarida bayan wancan furuci da yayi, ya kuma bar wajen ba tare da kara cewa komai ba.

KARANTA WANNAN: Takarar shugaban kasa 2023: Tambuwal ya nemi shawarar Obasanjo, Mark da Danjuma

Babbar magana: Shugaban kasa ya yi barazanar dukan dan jarida
Babbar magana: Shugaban kasa ya yi barazanar dukan dan jarida
Asali: Twitter

Dan jaridar O Globo ya tambayi shugaban kasar akan gaskiyar rahoton jaridar Crusoe da ke alakanta uwar gidansa Michelle Bolsonaro da Fabrício Queiroz, tsohon dan sanda.

Fabrício Queiroz babban abokin shugaban kasar ne, kuma tsohon hadimin yaronta ne Flavio Bolsonaro, wanda a yanzu sanata ne.

Queiroz da Flavio Bolsonaro na karkashin bincike kan wani shiri da ake zargin gwamnati na biyan ma'aikata kudi lokacin Flavio na dan majalisa a Rio de Janeiro, kafin Jair Bolsonaro ya zama shugaban kasa a Janairu 2019.

A cewar jaridar, Queiroz ya ajiye kudi a wani asusu da sunan Michelle Bosonaro daga shekarar 2011 da 2016.

Sai dai uwar gidan shugaban kasar har yanzu ba ta ce komai dangane da wannan zargi ba.

Jim kadan bayan da shugaban kasar ya yi barazanar dukan dan jaridar, kamfanin watsa labarai na O Globo ya fitar da sanarwa mai taken "fushi da fushin wani ... akan dan jarida daga kamfaninmu, wanda ya ke bakin aikinsa."

Irin wannan barazanar "na nuni da cewa Jair Bolsonaro baya mutunta ma'aikata ... wanda zai rinka fayyacewa al'umma gaskiya."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel