Takarar shugaban kasa 2023: Tambuwal ya nemi shawarar Obasanjo, Mark da Danjuma

Takarar shugaban kasa 2023: Tambuwal ya nemi shawarar Obasanjo, Mark da Danjuma

- Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya fara tuntuba da neman shawarwarin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023

- Tambuwal na son tsayawa takarar ne karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP)

- Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan jihar Sokoton ya gana da Obasanjo, David Mark da kuma tsohon ministan tsaro Danjuma

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya fara tuntuba da neman shawarwari daga manyan 'yan siyasa dangane da kudurinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Tambuwal na son tsayawa takarar ne karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wacce ta yi takara a cikinta a zaben fitar da gwani na 2019.

Jaridar THISDAY ta ruwaito cewa ya fara tuntuba da neman shawarwarin ne a ranar Alhamis lokacin da ya hadu da tsohon shugaban majalisar dattijai, David Mark.

Tambuwal a ranar Asabar ya kaiwa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ziyara da kuma tsohon ministan tsaro, Lt. Gen. Theophilus Danjuma (mai ritaya).

Gwamnan ya sa labule da Obasanjo na tsawon awa daya a babban ginin bincike da ajiye littattafai na shugaban kasa da ya gina a Abeokuta.

KARANTA WANNAN: Kwamishinan lafiya na jihar Lagos ya kamu da cutar COVID-19

Takarar shugaban kasa 2023: Tambuwal ya nemi shawarar Obasanjo, Mark da Danjuma
Takarar shugaban kasa 2023: Tambuwal ya nemi shawarar Obasanjo, Mark da Danjuma
Asali: UGC

Wata sanarwa daga hadimin Obasanjo ta fuskar watsa labarai, Mr. Kehinde Akinyemi, ya ruwaito gwamnan yana cewa ya ziyarci Obasanjo ne don tattauna batutuwan mulkin kasar.

"Mun san Baba jagoranmu ne, mai fada a ji. Dole ne mu zo mu duba yadda yake, mu kuma tuntube shi kan abubuwan da suka shafi mulkin kasar. Shine dalilin zuwanmu yau.

"Kuma munzo mu isar masa da gaisuwar al'ummar jihar Sokoto," kamar yadda sanarwar ta ruwaito.

Sai dai THISDAY a ranar Lahadi ta gano cewa makasudin ziyarar Tambuwal wajen Obasanjo shine neman shawara kan kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Majiya ta shaidawa jaridar cewa bayan haduwa da Obasanjo, Tambuwal ya garzaya birnin Lagos inda ya gana da Danjuma a gidansa.

Rahotanni sun bayyana cewa ya yiwa tsohon ministan bayani kan burinsa na yin takarar shugaban kasar karkashin jam'iyyar PDP.

Haka zalika bincike ya nuna cewa Tambuwal a ranar Alhamis ya gana da Mark a gidansa da ke Abuja, duk a cikin tuntuba da neman shawarwari da yake yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel