Yanzu-yanzu: Kwamishinan lafiya na jihar Lagos ya kamu da cutar COVID-19

Yanzu-yanzu: Kwamishinan lafiya na jihar Lagos ya kamu da cutar COVID-19

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Lagos, Farfesa Akin Abayomi, ya kamu da cutar mashako, wato COVID-19. Kwamishinan watsa labarai da tsare tsare na jihar, Gbenga Omotoso ne ya sanar da haka a ranar Litinin.

Sanarwar mai taken 'Sakamakon gwajin cutar COVID-19 na kwamishinan lafiya na jihar Lagos, Farfesa Akin Abayomi'.

Sanarwar ta ce: "Bayan yin alaka da marasa lafiya, da kuma yi masa gwajin COVID-19, sakamakon gwajin ya nuna cewa kwamishinan lafiyar ya kamu da cutar.

"Farfesa Akin Abayomi ya san matsayar lafiyarsa bayan da aka bi matakan gwaji da kuma bin diddigin wadanda ya yi mu'amala da su.

DA DUMINSA: APC ta lashe kujerun kananan hukumomi 18 a jihar Ondo

Yanzu-yanzu: Kwamishinan lafiya na jihar Lagos ya kamu da cutar COVID-19
Yanzu-yanzu: Kwamishinan lafiya na jihar Lagos ya kamu da cutar COVID-19
Asali: Twitter

"Sai dai, yana cikin koshin lafiya. Bisa bin tsarin killacewa a gida, kwamishinan lafiya na jihar zai zauna a gida na tsawon kwanaki 14, amma zaici gaba da yin ayyukansa a gidan.

"Addu'armu na tare da shi da iyalansa a wannan lokacin da zai killace kansa."

A raar Lahadi, hukumar dakile cututtuka ta kasa NCDC ta sanar da cewa sabbin mutane 322 ne suka kamu da CODI-19, adadin da ya kai 52,227.

Hukumar ta sanar da cewa mutane 1,002 ne suka rasa rayukansu a fadin kasar sakamakon kamuwa da cutar.

A cewar hukumar, mutane biyar ne suka mutu daga cutar a tsakanin awanni 24.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel