Taya murna: Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya cika shekaru 59 da haihuwa

Taya murna: Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya cika shekaru 59 da haihuwa

- Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya cika shekaru 59 da haihuwa.

- An haifi Sarkin ne a ranar 21 ga watan Agustan 1961

- Aminu Ado Bayero shine Sarkin Kano na 15 daga kabilar Fulanin Sullubawa, ya hau karagar mulki ne a ranar 9 ga watan Maris 2020

A ranar Juma'a 21 ga watan Agusta 2020, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya cika shekaru 59 da haihuwa. An haifi Sarkin ne a ranar 21 ga watan Agustan 1961.

Aminu Ado Bayero shine Sarkin Kano na 15 daga kabilar Fulanin Sullubawa, ya hau karagar mulki ne a ranar 9 ga watan Maris, biyo bayan tsige tsohon Sarki Muhammadu Sanusi na II.

Aminu Ado Bayero an haife shi a 1961. Mahaifinsa, Ado Bayero, shine Sarkin Kano daga shekarar 1963 zuwa shekarar 2014 kuma shine Sarki mafi dadewa a karagar Sarautar jihar.

Aminu shine d'a na biyu a wajen mahaifinsu. Sunan yayansa Sanusi Ado Bayero, da kuma Nasiru Ado Bayero, Sarkin Bichi na yanzu.

Muhammdu Sanusi na II, d'a ne a wajen dan uwan Aminu, shi ne kuma ya gaji mahaifinsa a mulkin Kano daga 2014 zuwa 2020 a lokacin da gwamnatin Kano ta tsige shi.

Aminu Ado ya yi karatun Firamare a Kofar Kudu, daga nan ya wuce jami'ar BUK, sai ya zarce kwalejin koyon tukin jirgin sama da ke Oakland, birnin Kalifoniya, kasar Amurka.

Ya yi bautar kasarsa a gidan talabijin mallakin gwamnatin Nigeria (NTA) a Makurdi.

KARANTA WANNAN: Dalilin da ya sa APC za ta samu nasara a zaben Ondo - Sanwo-Olu

Taya murna: Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya cika shekaru 59 da haihuwa
Taya murna: Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya cika shekaru 59 da haihuwa
Asali: Twitter

Bayero ya fara aikinsa ne a matsayin jami'in hulda da jama'a na kamfanin jirgin sama na Kabo Air, kafin ya zama injiniyan jirgi.

A shekarar 1990, an danashi Dan Majen Kano kuma hakimin Dala, a lokacin mulkin mahaifinsa, Ado Bayero, kafin a mayar da shi Dan Buram din Kano a watan Oktobar wannan shekarar.

A 1992, ya samu karin matsayi zuwa Turakin Kano kuma Sarkin Dawakin Tsakar Gida na Kano a 2000. Ya kuma taba rike mukamin shugaban kwamitin nada rawanin Sarkin Kano.

A shekarar 2014, Sarkin Kano na wancan lokaci, Muhammad Sanusi II, ya kara masa matsayi zuwa Wamban Kano, don haka, aka mayar da shi zuwa Kano ta tsakiya daga Dala.

Zuwansa Kano ta tsakiya ne ya sa ya maye gurbin Galadiman Kano, Alhaji Tijani Hashim, a matsayin hakimi.

A shekarar 2019, gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya nada shi Sarkin Bichi, inda daga bisani, bayan tsige Sunusi, aka nada shi Sarkin Kano na 15.

Ga wasu hotuna da aka dauke su a lokuta daban daban, bayan zamansa Sarkin Kano.

Taya murna: Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya cika shekaru 59 da haihuwa
Taya murna: Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya cika shekaru 59 da haihuwa
Asali: Twitter

Taya murna: Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya cika shekaru 59 da haihuwa
Taya murna: Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya cika shekaru 59 da haihuwa
Asali: Twitter

Taya murna: Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya cika shekaru 59 da haihuwa
Taya murna: Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya cika shekaru 59 da haihuwa
Asali: Twitter

Taya murna: Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya cika shekaru 59 da haihuwa
Taya murna: Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya cika shekaru 59 da haihuwa
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel