Lokaci ya yi: Tsohon ministan ayyuka, Olufemi Olumide ya bakunci lahira

Lokaci ya yi: Tsohon ministan ayyuka, Olufemi Olumide ya bakunci lahira

Rahoton da Legit.ng Hausa ta samu daga jaridar The Nation na nuni da cewa tsohon ministan ayyuka na Nigeria, Real Admiral Olufemi Olumide (mai ritaya) ya riga mu gidan gaskiya.

Tsohon ministan ya rasu ne bayan fama da gajeriyar rashin lafiya a Abeokuta, babban birnin jihar Lagos.

Ya rasu yana da shekaru 82.

Olumide, wanda ya kasance Injiniya, ya kuma kasance shugaban cibiyar ilimin tsare tsare na kasa da ke Jos.

Ya rike mukamai da yawa a rundunar sojin ruwa kafin lokacin ajiye aikinsa, tun a shekaru arba'in baya.

Olumide ya kasance babban jami'i mai rike da tuta, a sansanin sojin ruwa na gabar tekun Lagos, sannan ya rike mukamin Shugaban sashen matiriyal, a shelkwatar sojin ruwa, Lagos.

A cewar wata sanarwa daga iyalansa, za a binne gawar tsohon ministan a Abeokuta, mako mai zuwa.

KARANTA WANNAN: Duk da tsufana, zan so na zarce shekaru 100 a duniya - Obasanjo

Lokaci ya yi: Tsohon ministan ayyuka, Olufemi Olumide ya bakunci lahira
Lokaci ya yi: Tsohon ministan ayyuka, Olufemi Olumide ya bakunci lahira
Asali: Twitter

A wani labarin, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce da Allah zai karbi addu'arsa, to da zaiso ya rayu sama da shekaru 100 a duniya.

Ya ce yana so ya yi wannan doguwar rayuwar ne domin samun damar taya Sarkin Gbagura (Agura), Oba Sabur Bakare, Jamolu II murnar cika shekaru 20 a karagar mulki.

Obasanjo na daga cikin manyan bakin da suka halarci bukin murnar cikar sarkin shekara daya akan karar mulki, a garin Abeokuta, a ranar Talata.

Oba Bakare ya karbi sandar girma daga hannun tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, a ranar 21 ga watan Mayu, 2019, a matsayin Sarkin Gbagura na 9, a masarautar Egabaland.

Sarkin a yayin wannan bukin murna ya gabatar da taron addu'o'i na kowanne addini da kuma bukin bude wani fanfon tuka-tuka da ya ginawa wani gari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel