Tserewar mai laifi: Matasa sun yi wa 'yan sanda ruwan duwatsu yayin zanga-zanga

Tserewar mai laifi: Matasa sun yi wa 'yan sanda ruwan duwatsu yayin zanga-zanga

Daruruwan fusatattun matasa a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar Laraba suka rufe titunan da ke gaban hedkwatar 'yan sanda da ke Eleyele a Ibadan.

Matasan sun tada zanga-zangar ne sakamakon tserewar wani wanda ake zargi da kashe mutane a karamar hukumar Akinyele ta jihar.

Suna bukatar a tsananta bincike a kan lamarin tare da hukunta duk wani dan sanda da ke da hannu, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Sakamakon zanga-zangar, an samu cushewar hanyar tsakanin hedkwatar 'yan sandan da kuma tashar motar Eleyele.

Ganau ba jiyau ba, sun sanar da manema labarai cewa masu zanga-zangar sun matukar fusata kuma sun dinga jifan 'yan sandan da duwatsu tare da wasu makamai masu hatsari.

Wasu masu zanga-zangar, wadanda da yawa daga ciki dalibai ne na gaba da sakandare, suna dauke da fastoci inda suka yi tattaki har zuwa hedkwatar 'yan sandan da ke yankin Eleyele.

A yayin jawabi ga fusatattun matasan, kwamishinan 'yan sandan jihar, Nwachukwu Enwonwu, ya tabbatar da cewa za a damko wanda ake zargin tare da gurfanar da shi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Olugbenga Fadeyi, ya ce wasu daliban sun yi zanga-zangar a babban ofishin 'yan sandan jihar.

Fadeyi ya ce: "Kwamishinan 'yan sanda da sauran manyan jami'a sun sauraresu kuma sun amsa musu tambayoyinsu.

"Kun san daliban yanzu dai, wasu mun kasa shawo kansu amma mun yi jarumtar shawo kansu sakamakon kwarewarmu.

"Tuni sun koma."

Tserewar mai laifi: Matasa sun yi wa 'yan sanda ruwan duwatsu yayin zanga-zanga
Tserewar mai laifi: Matasa sun yi wa 'yan sanda ruwan duwatsu yayin zanga-zanga. Hpto daga the Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon matar da ta haifa 'ya'ya 44 a yayin da ta cika shekaru 40

A wani labari na daban, jami'an rundunar 'yan sandan jihar Legas sun damke wani mutum da ke ikirarin zama basarake mai shekaru 72 mai suna Lateef Olarinde, dan shi da wasu mutum uku a kan zarginsu da ake da kashe-kashe tare da wasu ayyukan tada tarzoma a birnin Oguntedo da ke jihar.

Sauran mutum hudun sun hada da Yusuf Olarinde mai shekaru 38, Kazeem Sadiku mai shekaru 35, Sanni Olarinde mai shekaru 37, Ayomide da Babatunde Lateef.

Kamensu ya biyo bayan korafe-korafen mazauna yankin a kan miyagun ayyukan Olarinde da sauran 'yan kungiyarsa da kuma umarnin da 'yan sandan suka samu daga kwamishinan 'yan sandan jihar, Hakeem Odumosu, na su damko wadanda ake zargi.

Jami'an 'yan sandan sun ce Olarinde ya kasance cikin wadanda ake nema ido rufe a yankin, sakamakon kisan kai da tada tarzoma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel