Duk da tsufana, zan so na zarce shekaru 100 a duniya - Obasanjo
- Chief Olusegun Obasanjo ya ce da Allah zai karbi addu'arsa, to da zaiso ya rayu sama da shekaru 100 a duniya
- Obasanjo, wanda yake da shekaru 83 a wannan shekarar, ya ce zai so ace ya ga ranar da Sarkin Gbagura zai cika shekaru 20 a karagar mulki
- Agura Bakare, ya nuna jin dadinsa tare da cewa hadin kan masu rike da sarautun gargajiya zai kawo ci gaba a kasar Yarabawa
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce da Allah zai karbi addu'arsa, to da zaiso ya rayu sama da shekaru 100 a duniya.
Ya ce yana so ya yi wannan doguwar rayuwar ne domin samun damar taya Sarkin Gbagura (Agura), Oba Sabur Bakare, Jamolu II murnar cika shekaru 20 a karagar mulki.
Obasanjo na daga cikin manyan bakin da suka halarci bukin murnar cikar sarkin shekara daya akan karar mulki, a garin Abeokuta, a ranar Talata.
Oba Bakare ya karbi sandar girma daga hannun tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, a ranar 21 ga watan Mayu, 2019, a matsayin Sarkin Gbagura na 9, a masarautar Egabaland.
Sarkin a yayin wannan bukin murna ya gabatar da taron addu'o'i na kowanne addini da kuma bukin bude wani fanfon tuka-tuka da ya ginawa wani gari.
Obasanjo, wanda yake da shekaru 83 a wannan shekarar, yayin da yake jawabi a taron addu'o'in, ya ce zai so ace ya ga ranar da Sarkin zai cika shekaru 20 a saman karagar mulki.
KARANTA WANNAN: Sheik Zakzaky ya raba magunguna da gidajen sauro a sansanonin 'yan gudun hijira

Asali: UGC
Ya ce, "Zan kasance a nan ranar da ka cika shekaru 20 a karagar mulki, ko an gayyace ni ko ba a gayyace ni ba.
"A lokacin da ka cika shekaru 20 a karagar mulki, idan har Allah ya amsa addu'ata, to sai kuga Allah ya sa na zo taron, lokacin ina da sama da shekaru 100 a duniya."
Tsohon shugaban kasar, ya kuma shawarci basaraken da ya ci gaba da da'awar zaman lafiya da hadin kai a tsakanin masu sarautun gargajiya na kasar Yarabawa.
"Akwai lokuta da yawa da Kabiyesi ke jin magana akwai lokutan da baya jin magana. Idan har muka hada kai, babu abunda ba zamu iya yi ba a kasar Yarabawa da ma Nigeria," cewar Obasanjo.
A nashi jawabin Alake na kasar Egbaland, Oba Adedotun Gbadebo, ya yi nuni da cewa a shekara daya ta Oba Bakare ta kawo hadin kai a tsakanin masu rike da sarautun gargajiya, shuwagabanni, masu da tsaki da sauran jama'a na kasar Egba.
Agura Bakare, ya nuna jin dadinsa aka dangon farin jama'ar da ya gani, yana mai cewa hadin kai da soyayya tsakanin al'ummar Egba zai ci gaba da dorewa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng