Hotuna da bidiyon matar da ta haifa 'ya'ya 44 a yayin da ta cika shekaru 40

Hotuna da bidiyon matar da ta haifa 'ya'ya 44 a yayin da ta cika shekaru 40

- Wata mata mai suna Mariam Nabatanzi ta bayyana a mace mafi albarkar haihuwa a kasar Uganda

- Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Nabatanzi ta haifa 'ya'ya 44 kuma dukkan yaran ta haifesu ne kafin ta cika shekaru 40 a duniya

- An san mata a nahiyar Afrika da haihuwar yara saboda da yawa a nahiyar ana son tara iyali

A zamanin nan, ma'aurata kan haifa yara daya ko biyu, amma wannan matar 'yar asalin kasar Uganda ta kasance matar da ta fi kowa albarkar haihuwa. Ta haifa 'ya'ya 44 kafin ta cika shekaru 40 a duniya.

Sunanta Mariam Nabatanzi kuma tana zama a Kabimbiri a kasar Uganda. Ta hau kanun labarai saboda haihuwarta.

Kamar yadda OddityCentral ta ruwaito, matar ta haifa 'ya'ya 44 kafin ta cika shekaru 40 a duniya.

Legit.ng ta gano cewa, matar ta haifa tagwaye sau shida, 'yan uku sau hudu, 'yan hudu sau uku. Ta kuma haifa daddaya sau da yawa.

Hotuna da bidiyon matar da ta haifa 'ya'ya 44 a yayin da ta cika shekaru 40
Hotuna da bidiyon matar da ta haifa 'ya'ya 44 a yayin da ta cika shekaru 40. Hoto daga OddentyCentral
Asali: UGC

Amma kuma wasu daga cikin 'ya'yanta sun rasu kuma 38 ne kadai suke raye.

Duk da yawan iyalanta wadanda ke rayuwa a gida daya, matar mai shekaru 40 wacce bata da miji ce ke ciyar da iyalan.

Nabatanzi ta yi aure a lokacin da take da shekaru 12 kuma mijinta na da shekaru 40. Matar ta tsallake rijiyar mutuwa yayin da kishiyar mahaifiyarta ta yi yunkurin kasheta ta hanyar saka mata kananan gilasai a cikin abinci.

Hotunan matar da ta haifa 'ya'ya 44 a yayin da ta cika shekaru 40
Hotunan matar da ta haifa 'ya'ya 44 a yayin da ta cika shekaru 40. Hoto daga OddityCentral
Asali: UGC

KU KARANTA: Kisan kai: 'Yan sanda sun damke basarake, 'ya'yansa 2 da kungiyarsa ta daba

Kamar yadda Nabatanzi ta ce, matar mahaifinta ta kashe kannanta hudu ta wannan hanyar. Ta ce ta tsallake sharrinta ne lokacin da ta yi aure.

Ta ce ta fada auren amma na cin zarafi. Nabatanzi ta ce mijinta ya na da mata da yawa da 'ya'ya wadanda Nabatanzi ta dinga kula da su.

Ta haifa tagwayenta na farko a 1994 lokacin da take da shekaru 13.

A wani labari, wata mata mai suna Lucy Kelsall ta rasa mijinta mai suna David sakamakon kansar makogwaro. Daga baya ta haifa tagwaye bayan shekaru uku da mutuwarsa.

Mijin Lucy ya bada maniyyinsa kafin ya fara ciwo.

Matar mai shekaru 37 wacce mijinta ya rasu a 2017, ta ce har yanzu tana farin cikin cewa tana da ragowar mijinta wanda aka saka mata a mahaifa kuma ta haifesu.

Ta haifa tagwaye biyu masu suna David da Samuel, bayan an saka mata maniyyinsa a mahaifarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel