Da duminsa: Shugaban kasar Mali, Ibrahim Keita, ya yi murabus

Da duminsa: Shugaban kasar Mali, Ibrahim Keita, ya yi murabus

Shugaban kasar Mali a ranar Laraba ya ce ya yi murabus domin hana "zubar da jini", awanni bayan da rundunar soji suka yi caraf da shi, a yunkurin juyin mulki. Cafke shugaban kasar da yunkurin juyin mulkin, yana zuwa ne bayan shafe sama da watanni ana rikicin siyasa a kasar Mali.

Sojojin hamayya sun cafke Ibrahim Boubacar Keita da Firam Minista Boubou Cisse a ranar Talata, tare da tsaresu a wani sansanin soji da ke garin Kati, kusa da Bamako, babban birnin kasar.

Dandanzon mutane ne suka taru don nuna murnarsu na tsare Keita, tare da bukatar dole sai yayi murabus, a lokacin da sojojin suka kutsa kai gidan tsohon shugaban kasar.

Keita ya bayyana gaban talabijin mallakin kasar a daren ranar Laraba domin sanar da murabus din gwamnatinsa da majalisar tarayya, kuma murabus din zai fara aiki nan take.

"Idan har hakan zai faranta ran wasu tsiraru daga rundunar soji, to shi kenan, na kawo karshen tababar, ina ma da wani zabi ne?" ya bayyana.

"Dole ne na mika wuya, saboda bana son a zubar da jini."

KARANTA WANNAN: ASUU ta zabi tsarin UTAS akan IPPIS na gwamnatin tarayya

Da duminsa: Shugaban kasar Mali, Ibrahim Keita, ya yi murabus
Da duminsa: Shugaban kasar Mali, Ibrahim Keita, ya yi murabus
Asali: UGC

Sai dai babu tabbacin ko har yanzu Keita na tsare a sansanin soji na Kati, wanda kuma a nan garin ne dai ya karbi mulki a shekarar 2012.

Makwaftan kasashe, Faransa da kungiyar hadakar kasashen turai ta yi gargadi kan bayar da mulki ba bisa ka'ida ba a yayin da aka yi juyin mulkin ranar Talata.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci da a gaggauta sakin Keita da Cisse a yayin da 'yan diflomasiyyar birnin New York suka ce majalisar tsaro zata yi zama kan lamarin.

Kungiyar hadakar kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) sun yi Allah-wadai da wannan juyin mulkin, inda har sukayi barazanar rufe iyakokin kasashen da ke makwaftaka da Mali.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel