Da duminsa: ASUU ta zabi tsarin UTAS akan IPPIS na gwamnatin tarayya

Da duminsa: ASUU ta zabi tsarin UTAS akan IPPIS na gwamnatin tarayya

- Kungiyar ASUU ta sanarwa gwamnatin tarayya cewa ta zabi amfani da tsarin UTAS wajen biyan albashi

- ASUU ta zabi tsarin UTAS ne domin ya zama kishiyar tsarin da gwamnatin ta gabatar na IPPIS

- Haka zalika kungiyar ta ce ba zata janye daga yajin aikin da take yi ba har sai gwamnatin tarayya ta amince da bukatarsu ta 2019

Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa ASUU a ranar Talata ta sanarwa gwamnatin tarayya cewa ta zabi amfani da tsarin 'University Transparency and Accountability Solution' wajen biyan albashi.

Kungiyar ta ce ta zabi tsarin UTAS ne domin ya zama kishiyar tsarin da gwamnatin ta gabatar na IPPIS, tana mai nuni da cewa sabon tsarin zai fi dacewa da su.

A cewar ASUU, manhajar UTAS an kammalata kuma an gabatar da ita ga ma'aikatar Ilimi da sashen manyan ma'aikata na ma'aiktar.

Daga cikin manyan jami'an akwai babban sakataren hukumasr jami'o'i na kasa, Farfesa Abdulrasheed Abubakar, inda suka nuna manhajar a ranar Litinin.

KARANTA WANNAN: Batanci ga Annabi: Kungiyar CAN ta goyi bayan rataye Yahaya Aminu Sharif

Da duminsa: ASUU ta zabi tsarin UTAS akan IPPIS na gwamnatin tarayya
Da duminsa: ASUU ta zabi tsarin UTAS akan IPPIS na gwamnatin tarayya
Asali: Twitter

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya bayyana hakan a taron manema labarai a jami'ar Abuja da ke Gwagwala, daga cikin mahalarta taron akwai manyan shuwagabanni.

Sai dai Ogunyemi ya yi nuni da cewa kungiyar ba zata janye daga yajin aikin da take yi ba har sai gwamnatin tarayya ta amince da bukatarsu ta 2019.

"Muna fatan gwamnati za ta cika mana bukatunmu saboda amfanin tsarin UTAS ga jami'o'i na gwamnati da na kudi ba zai samu a cikin kowacce manhaja a Nigeria ba.

"A yanzu da kungiyar ta kusa kammala komai na samar da kishiyar IPPIS, muna fatan cewa gwamnatin za ta cika alkawarinta a wannan lokacin da muke yajin aiki," a cewarsa.

Shugaban kungiyar ASUU ya kuma har yanzu gwamnati bata biya malaman jami'ar Maidugir da jami'ar noma ta Michael Okpara da ke Umudike ba.

A cewarsa, babban akanta na kasa ne ya dakatar da albashin nasu saboda sun ki amincewa suyi rejista da tsarin IPPIS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel