Batanci ga Annabi: Kungiyar CAN ta goyi bayan rataye Yahaya Aminu Sharif

Batanci ga Annabi: Kungiyar CAN ta goyi bayan rataye Yahaya Aminu Sharif

- Kungiyar CAN reshen jihar Kano ta bayyana matsayarta kan hukuncin kisa da aka yankewa mawaki a Kano, Yahaya Aminu Sharif

- Kungiyar ta ce hukuncin da kotun Shari'ar ta yanke ya yi dai dai da addinin Musulunci

- Adeyemo ya yi nuni da cewa a addinin Kiristanci, cin mutunci ne furta kalaman batanci ga ruhi mai tsarki, zunubin da ba za a taba yafewa ba

Kungiyar mabiya addinin Kirista ta kasa CAN reshen jihar Kano ta magantu kan hukuncin kisa da aka yankewa mawaki a Kano, Yahaya Aminu Sharif.

Idan ba a manta ba wata kotun Shari'a a Kano, ta yankewa Sharif hukuncin kisa sakamakon kamashi da laifin yin batanci ga Annabi a cikin wasu wakokinsa.

Da yake magana kan lamarin da ya jawo kumfar baki, Adeolu Samuel Adeyemo, shugaban kungiyar CAN na jihar Kano yace kungiyar ba ta da jayayya kan lamarin tunda an yanke hukuncin bisa shari'ar Musulunci.

Ya ce: "Mu a bangarenmu na CAN, hukuncin da kotun Shari'ar ta yanke ya yi dai dai da addinin Musulunci don haka bamu da jayayya tunda dai bai sabawa Musulunci ba."

KARANTA WANNAN: Zaben Ondo: Dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar PDP ya zabi abokin takararsa

Batanci ga Annabi: Kungiyar CAN ta goyi bayan rataye Yahaya Aminu Sharif
Batanci ga Annabi: Kungiyar CAN ta goyi bayan rataye Yahaya Aminu Sharif
Asali: Twitter

Adeyemo ya yi nuni da cewa a addinin Kiristanci, cin mutunci ne furta kalaman batanci ga ruhi mai tsarki, zunubin da ba za a taba yafewa ba.

Ya kara da cewa da wannan ilimin, tsoma baki kan hukuncin da Shari'ar Musulunci ta zartas ba abu ne mai yiyuwa ba.

A cewar shugaban kungiyar ta CAN, "A yanzu, idan kana son sanin matsayar addinin Kiristanci akan batanci, zan ce maka akwai kalaman da zaka iya furtawa akwai wadanda basu dace ba.

"Kuma Yesu ya ce batanci ga ruhi mai tsarki babban zunubi ne da ba a yafewa. Wannan shine matsayar addinin Kirista."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel