Ba zan iya jure ganin mijina da wata macen ba - Matar aure ga kotu

Ba zan iya jure ganin mijina da wata macen ba - Matar aure ga kotu

Wata malamar makaranta mai suna Idowu Oluokun a ranar Talata ta sanar da wata kotun gargajiya da ke Mapo a Ibadan, da ta tsinke igiyar aurenta mai shekaru 16 da mijinta Oyetunji saboda kishiyar da yayi mata.

Idowu ta sanar da hakan ne a yayin da take bayani a gaban Mai shari'a Ademola Odunade, alkalin kotun. Ta kara da cewa mijinta ba abun yarda bane.

Ta kara da cewa, bayan ta haihu da Oyetunji, ya sanar da ita cewa ya aura wata mata wacce 'yan uwansa suka fi so saboda daga yankinsu take.

"Ya sanar da ni cewa ya yanke hukuncin raba mana kwana da sabuwar amaryarsa.

"Na matukar fusata saboda ba wannan bane yarjejeniyar mu ta farko kuma ba zan iya jure wannan abun kunyar ba.

"Na bukaci Oyetunji da ya koma wurin amaryarsa saboda ba zan iya karba-karba da ita ba.

"Tun bayan nan, Oyetunji ya daina kula da danmu har sai cikin kwanakin nan da ya zo zai karba dan shi.

"Ya aiko N30,000 don biyan kudin jarabawar kammala sakandare ta danmu, amma kuma bai san yadda ya yi har ya shiga jami'a ba.

"Idan kotu ta amince ya karba danmu, ina bukatar ya biya ni duk abinda na kashe na tsawon shekaru 16," Idowu ta ce.

Ba zan iya jure ganin mijina da wata macen ba - Matar aure ga kotu
Ba zan iya jure ganin mijina da wata macen ba - Matar aure ga kotu. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ka fada wa jama'a malaman da ke son kudi ko ka rufe mana baki - Fasto ya caccaki El-Rufai

Tun farko, Olatunji mazaunin Ogbomoso, ya bayyana rashin soyayya, rashin yarda da kuma miyagun halaye a matsayin abinda ya sa ya nemi saki.

"Mai shari'a, a bayyane yake Idowu bata kaunata. Na daina kashe musu kudi ne a shekarar da ta gabata saboda yadda take karbar kudi mai yawa a hannuna.

"Na san cewa N17,000 ake biya a makarantar gwamnati don jarabawar kammala sakandare amma Idowu ta ce N30,000 kuma na tura mata.

"Yaron ya bayyana cewa yana son zama tare da ni amma tana hana shi," Oyetunji ya ce.

Amma kuma Oyetunji ya ki yin tsokaci a kan zargin da Idowu take masa.

A hukuncin alkalin, Odunade ya kalubalanci yadda mai karar ya yi watsi da matarsa saboda wata kuma ya dawo yana son karbar dan su daya.

Ya tsinke igiyar aurensu inda ya bai wa Idowu damar rike dan ta.

Odunade ya bai wa Oyetunji umarnin biyan N10,000 duk wata don ciyar da yaron kuma ya dauka nauyin karatunsa da wasu bukatunsa na walwala.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel