COVID-19: Gwamnatin tarayya ta magantu kan ranar bude jami'o'i

COVID-19: Gwamnatin tarayya ta magantu kan ranar bude jami'o'i

- Gwamnatin tarayya ta magantu kan ranar bude makarantu gaba daya da suka hada da jami'o'i

- Boss Mustapha ya ce kwamitin yaki da COVID-19 a kasar ya yi farin ciki na yadda makarantun suke kiyaye dokoki a yayin zana jarabawar WAEC

- Ya roki dalibai da su kwantar da hankalunansu na cewar da zaran an samu tabbacin komai ya dai daita, to za a bude makarantun

Gwamnatin tarayya ta ba kungiyar dalibai ta kasa (NANS) tabbacin cewa za a bude makarantu da suka hada da jami'o'i da zan an samu damar yin hakan.

Shugaban kwamitin yaki da COVID-19 na kasa kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bada tabbacin a wani taron bita na kwamitin a ranar Litinin.

Ya ce a ranar Litinin dalibai suka fara zana jabawarar kammala makarantar sakandire, kuma kwamitin PTF na farin ciki na yadda makarantun suke kiyaye dokoki.

Da wannan ne ya yi kira ga kungiyar daliban ta NANS da su kwantar da hankalunansu na cewar da zaran an samu tabbacin komai ya dai daita, to za a bude makarantun.

NANS a makonni biyu da suka wuce, ta yi nuni da cewa kasashen duniya ne suka fuskanci annobar COVID-19, don haka Nigeria ta samar da mafita, don bude makarantu.

KARANTA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta cafke masu garkuwa da mutane 45 da suka addabi Borno

COVID-19: Gwamnatin tarayya ta magantu kan ranar bude jami'o'i
COVID-19: Gwamnatin tarayya ta magantu kan ranar bude jami'o'i
Asali: UGC

"Kwamitin PTF na farin ciki da wani tsari da kungiyar NANS ta kawo na samar da cibiyoyin daukar bayanan gwaji a kananan hukumominsu, tare da bukatar saura ma suyi koyi.

"Haka zalika, samar da cibiyoyin bayar da magani wanda ke taimakawa wajen samu yawan wadanda suke warkewa tare da rage yawan masu mutuwa abun a yabawa NANS ne.

"A yanzu, muna matakin dakile yaduwar a cikin garuruwa, kuma babban matakin da zamu dauka yanzu shine ci gaba da gwaji, idan an gano ayi magani."

Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta cafke mutane 45 da ake zarginsu da laifin garkuwa da mutane da mallakar miyagun makamai a sassa daban daban na jihar.

Daga cikin wadanda aka kama, akwai mai shekaru 40 wanda ake zargin ya kware wajen safarar makamai ga 'yan ta'addan Boko Haram.

Jihar Borno ta dade tana fuskantar matsalolin tsaro, inda aka kashe mutane da dama, ya yin da dubunnai suka rasa muhallansu na gado.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel