Na gaji da karfin iko da juya ni da mijina ke yi - Matar aure ga kotu

Na gaji da karfin iko da juya ni da mijina ke yi - Matar aure ga kotu

- Wata mata mai suna Damilola Osululu ta sanar da wata kotun gargajiya cewa ta gaji da iko da kuma yadda mijinta ke juya ta

- Akinwunmi Osululu, ya sanar da kotu cewa matarsa bata daukarsa da muhimmanci kamar kasuwancinta

- A duk lokacin da suka yi fada, ta kan dauka makami inda take kai masa hari kamar wasu 'yan daba

Wata mata 'yar kasuwa mai suna Damilola Osululu, a ranar Litinin, ta sanar da wata kotun gargajiya da zama a Ile-Tuntun, Mapo a Ibadan, a kan cewa ta gaji da mijinta.

Matar auren ta ce ba za ta iya jure iko da yadda mijinta ke juya ta ba saboda ta yi hakuri da shi na tsawon lokaci.

Damilola ta ce duk da tana son mijinta, kuma bata shirya rabuwa da shi ba, bata amince da irin halayyar da yake nuna mata ba.

Mijin nata mai suna Osululu Akinwumi, ya shigar da kara a gaban wata kotu domin neman rabuwa da Damilola. Ya ce bata jin magana kuma tana hararsa a wasu lokuta.

Ya ce ya gaji da gayyatar dangi don sasanta tsakaninsu idan rikici ya balle.

Na gaji da karfin iko da juya ni da mijina ke yi - Matar aure ga kotu
Na gaji da karfin iko da juya ni da mijina ke yi - Matar aure ga kotu. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Kotu ta soke zaben gwamnoni na jihar Bayelsa

Mai karar ya ce, "Bata jin magana. Ta fi yin imani da kasuwancinta fiye da mu. Duk lokacin da muka yi fada, tana amfani da makami wurin kai min hari.

"Ina tunatar da ita cewa mu ba 'yan daba bane. Bamu da kudin kai wa asibiti, don haka dole ne mu gujewa mugun tsautsayi. Amma bata dainawa.

"Na kai kararta wurin iyayenta sau babu adadi amma bata daina ba. Hakazalika, bata damu da yaranmu ba.

"Ba haka take ba lokacin muna soyayya. Ba zai yi dadi ba idan na mutu a wannan lokacin saboda akwai wadanda nake kula da su."

Damilola ta yi martani inda ta ce har yanzu tana son mijinta. Ta dauka alkawarin sauya hali idan kotun bata saurari bukatar mijinta ba.

Alkalin kotun, Henry Agbaje, ya yi kira ga ma'auratan da su sasanta kansu ko saboda haihuwar da suka yi. Ya ce auren shekaru uku bai dace ya kare ba.

Agbaje ya dage sauraron karar zuwa ranar 31 ga watan Augustan 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel