Yanzu-yanzu: Barcelona ta fatattaki Kocinta, Setien

Yanzu-yanzu: Barcelona ta fatattaki Kocinta, Setien

Babbar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona FC ta fatattaki manajanta, Quique Setien, bayan cin 8 da biyun da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta yi musu.

Kungiyar kwallon kafan ta sanar da sallamar kocin nata a wata takarda da ta fitar a shafinta na yanar gizo, jaridar The Nation ta wallafa.

Ta ce: "Majalisar daraktoci ta amince da sallamar Quique Setien. Don haka daga yanzu ya tashi daga kocinta.

"Wannan ne hukunci na farko da aka fara dauka yayin da ake fara kawo sabbin gyare-gyare a kungiyar wanda daraktocin suka aminta da ita. Za a sanar da sabon kocin nan da kwanaki kadan."

Setien ya samu matsuguni a kungiyar kwallon kafar ta Barca a ranar 13 ga watan Janairu bayan fatattakar kocinta Ernesto Valverde da ta yi.

Ba a yi tsammanin fatattakar kocin ba saboda shugaban kungiyar kwallon kafar, Bartomeu ya dauka alkawarin sauye-sauye bayan babbar rashin nasarar da ta samu.

Yanzu-yanzu: Barcelona ta fatattaki kocinta, Setien
Yanzu-yanzu: Barcelona ta fatattaki kocinta, Setien. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Batanci ga Allah: Kotu ta yanke wa yaro mai shekaru 13 hukunci mai tsanani

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel