FG ta gargadi masu bada cin hanci don kar ayi masu gwajin COVID-19 a tashar jirgin sama

FG ta gargadi masu bada cin hanci don kar ayi masu gwajin COVID-19 a tashar jirgin sama

- Hukumar FAAN ta gargadi fasinjojin da ke shigowa kasar dasu gujewa ba ma'aikatanta cin hanci da rashawa

- Akwai rade raden cewa fasinjojin da ke shigowa kasar na bada cin hancin N50,000 zuwa N100,000 domin gujewa killacewa da gwajin COVID-19

- Hukumar ta gargadi fasinjoji da su daina ba jami'anta cin hanci da rashawa, hakan zai iya kara yaduwar annobar COVID-19 a kasar

Hukumar kula da harkokin tashoshin jiragen sama ta kasa (FAAN), ta gargadi fasinjojin da ke shigowa kasar dasu gujewa ba ma'aikatanta cin hanci da rashawa.

Hukumar ta yi zargin cewa wasu jami'anta a Abuja na karbar kudade daga hannun masu shigowa kasar domin gujewa yi masu gwajin cutar COVID-19 da sauran bincike.

Haka zalika, FAAN ta fayyace cewa ba ta karbar kudaden fasinjoji da sunan yi masu aiki.

Hukumar ta magantu ne kan wani sako da ke zargin ma'aikatanta a tashar jirgin sama ta Nnamdi Azikiwe, Abuja da karbar N50,000 zuwa N100,000 domin tsallakar da mutum daga killacewa.

Amma a wata sanarwa daga Janar Manaja, sashen harkokin hukumar, Mrs. Henrietta Yakubu, ta ce hukumar ta gargadi fasinjoji kan cewar babu wani aiki da za ayi masu wanda zasu biya kudi.

KARANRA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta cafke masu garkuwa da mutane 45 da suka addabi Borno

FG ta gargadi masu bada cin hanci don kar ayi masu gwajin COVID-19 a tashar jirgin sama
FG ta gargadi masu bada cin hanci don kar ayi masu gwajin COVID-19 a tashar jirgin sama
Asali: UGC

Banda hakan, hukumar ta yi nuni da cewa duk fasinjojin da zasu shigo kasar sai an yi masu gwajin COVID-19 kafin su bar tashar jirgin da suke.

"Don haka, kada su biya kudi ga jami'anmu don tsallake wannan gwaji," a cewar hukumar.

Ta ce kasar ta bude tashoshin ne a mataki mataki, don haka fasinjoji su daina ba jami'ai cin hanci da rashawa, hakan zai iya kara yaduwar annobar COVID-19 a kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel