Caccakar Buratai a kan tsaro: Kotun soji za ta gurfanar da Kofur

Caccakar Buratai a kan tsaro: Kotun soji za ta gurfanar da Kofur

Martins Idakpini, soja mai mukamin Lance Corporal, wanda ya kalubanci Tukur Buratai, shugaban sojin kasa, an mayar da shi jihar Sokoto inda za a gurfanar da shi a gaban kotun soji.

Kotun ta sojoji ce kadai wacce dakarun kadai ake gurfanarwa a yayin da ake zarginsu da wani laifi.

An kama Idakpini kuma an garkamesa a Abuja bayan wani bidiyonsa da ya bulla inda yake zargin Buratai a kan nuna halin ko in kula a yayin yaki da ta'addanci a kasar nan.

A ranar Asabar, Akinyode, lauyan wanda ake zargi, ya ce ana cin zarafin sojan a yayin da yake tsare duk da rashin lafiya da yake fama da ita.

"Bayanan da ke samunmu a yanzu yana nuna cewa Kofur Martins an dauke shi daga Abuja zuwa Sokoto inda za a gurfanar da shi a gaban kotu a ranar Litinin," yace a wata takarda.

Ya kara da cewa, "An sanar da ni cewa rundunar na tirsasa masa wani lauya don kokarin yanke masa hukuncin da ba na shi bane.

Caccakar Buratai a kan tsaro: Kotun soji za ta gurfanar da Kofur
Caccakar Buratai a kan tsaro: Kotun soji za ta gurfanar da Kofur. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Hotunan kasaitacciyar liyafar da masarautar Ibira ta shiryawa Adama Indimi da angonta

"Kofur Martins ya matukar shan wahala kuma ana daukar shi kamar ba mutum ba. Ana hana shi abinci duk da cutar ulsa da yake da ita.

"Mun mika korafi ga AGF da shugaban rundunar don sanar da su umarnin kotu. Na kira AGF kuma ya tabbatar min da cewa za a bi dokar kotun. Ni da matarsa mun je ganinsa har sau uku amma ba a bar mu ba."

Wata kotun tarayya da ke Abuja a watan Yuli ta bada umarnin cewa a bar matar Idakpini, lauyansa da 'yan uwansa su dinga ganinsa.

Kotun ta sake umartar rundunar sojin da ta gujewa take hakkokin sojan a kowanne fanni.

Har a halin yanzu, kakakin rundunar sojin, Sagir Musa, bai yi martani a kan lamarin ba don ba a riga an samesa a waya ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel