Rage teba da amfani 9 na ganyen gwaiba ga lafiyar bil Adama

Rage teba da amfani 9 na ganyen gwaiba ga lafiyar bil Adama

Bayan kasancewarta daya daga cikin dangin kayan itatuwa da ake marmari, tabbas da yawan mutane kuma suna sane da masaniyar amfanin Gwaiba ga lafiyar su.

Kasashen duniya dama kamar Amurka, Sin, Masar, Indiya, Japan da kuma galibin kasashen bakar fata a nahiyyar Afrika, sun dauke shekaru aru-aru suna cin gajiyar maganin da ganyen gwaiba ke yi.

Binciken masana sirrin tsirrai da kuma na kimiya, sun dade da bayar da tabbaci na musamman kan alfanun ganyen gwaiba.

Sai dai kamar yadda bincike masana ya bayyana ba kowa ya san sirrikan da ganyen Gwaiba ya kunsa ba wajen kiwatar lafiya sakamakon sunadarai dake tattare cikin sa.

Ganyen Gwaiba yayin tafasa shi
Ganyen Gwaiba yayin tafasa shi
Asali: UGC

Ganyen Gwaiba ya kunshi tarin sunadai da masu yakar cututtuka iri-iri tare da inganta lafiya musamman a yayin da aka sarrafa kuma aka yi amfani da shi ta hanyoyin da suka dace.

Ganyen dan itaciyar yana dauke da wasu muhimman sunadarai masu zaman maganin cututtuka musamman wadanda aka sani a wannan zamani.

KARANTA KUMA: Zaben Edo: INEC za ta dauki ma'aikata 20,000 na wucin-gadi

Daga cikin sunadaran da ganyen gwaiba ya kunsa akwai; antioxidants, antibacterial da anti-inflammatory irin su polyphenols, carotenoids, flavonoids da kuma tannins dake da matukar bayar da tallafi wajen kawar da wasu cututtuka da dama.

Tasirai da wannan sunadarai suka kunsa tare da rawar da suke takawa wajen kiwatar lafiya sun hadar da;

1. Rage nauyin jiki

2. Tasiri ga cutar ciwon suga (diabetes)

3. Rage teba da daskararren maiko (Cholesterol)

4. Tsayar da amai da gudawa

5. Hana kamuwa da cutar nan ta hunhu da ake kira Bronchitis.

6. Waraka ga cututtukan hakori, makoshi da kuma dadashi.

7. Ciwon daji wato Kansa.

8. Habaka samar da ruwan maniyyi ga maza

9. Warkar da gulando.

10. Kawar da cutar fata musamman kyazbi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng