Sojin sama sun ragargaza sansanin ISWAP, sun kashe mayaka masu yawa

Sojin sama sun ragargaza sansanin ISWAP, sun kashe mayaka masu yawa

Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza wani sansanin mayakan ta'addanci na ISWAP da ke jihar Borno, majiya daga rundunar sojin ta tabbatar.

Kamar yadda shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche, ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a.

Ya ce sansanin 'yan ta'addan da ke Tongule a yankin tafkin Chadi da ke arewacin jihar Borno ya sha wuta daga dakarun Operation Lafiya Dole.

Enenche ya kara da cewa, sun kai samamen ne ta jiragen yaki a ranar Laraba bayan rahotonnin da suka samu daga jama'a, wanda ke nuna cewa akwai al'amuran 'yan ta'addan a kauyen.

Ya bayyana cewa, samamen na daga cikin kokarin kawo karshen ta'addanci a yankin arewa maso gabas. Hakan ya kawo karshen rayukan mayakan ISWAP a sansanin.

"Rundunar sojin saman Najeriyan ta tura jiragen yaki wadanda suka dinga ragargazar sansanin, hakan ya kawo tarwatsewar gidajen mayakan tare da kashe wasu daga ciki," takardar ta ce.

A bangarensa, shugaban rundunar sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar, ya jinjinawa kokari da kwarewar dakarun.

Ya yi kira garesu da su ci gaba da tsanantawa tare da matsawa 'yan ta'addan da ke dukkan fadin kasar nan.

KU KARANTA: Zargin gwamnan arewa da Boko Haram: Wurin 'yan kasuwar kauye na samu labari - Mailafiya

Sojin sama sun ragargaza sansanin ISWAP, sun kashe mayaka masu yawa
Sojin sama sun ragargaza sansanin ISWAP, sun kashe mayaka masu yawa. Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta sanar da cewa ta kashe wasu 'yan bindiga guda biyu tare da kubutar da mutane biyu da su ka sace a yankin karamar hukumar Dutsinma.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya aka rabawa manema labarai a Katsina.

Ya bayyana cewa an samu wannan nasara ne yayin da jami'an rundunar 'yan sanda a karkashin atisayen 'Puff Adder' su ka dira yankin bayan samun rahoton bullar 'yan bindiga dauke da bindigu.

A cewarsa, rundunar 'yan sanda ta samu labarin cewa 'yan bindiga dauke da bindigu samfurin AK 47 sun shiga kauyen Kwaro da ke yankin karamar hukumar Dutsinma a ranar 12 ga watan Agusta.

SP Isha ya kara da cewa 'yan bindigar sun kashe wani mutum mai suna Mohammed Auwal tare da sace wasu mutane biyu da dabbobi ma su yawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel