Labarin bogi: Kotu ta bai wa DSS umarnin ci gaba da tsare Matashi

Labarin bogi: Kotu ta bai wa DSS umarnin ci gaba da tsare Matashi

Wata kotun Majistare da ke zama a Lokoja ta dage sauraron wata shari'a zuwa ranar Talata, kafin duba bukatar belin wani Habib Rabiu mai shekaru 35, a kan zarginsa da ake da yada labaran bogi.

Idan za mu tuna, wanda ake zargin ya yi wallafa ta shafinsa na Facebook, inda ya ce zazzabi na kashe jama'a a jihar Kogi, lamarin da ya tada hankalin jama'ar jihar.

Kotun majistaren, wacce ta samu jagorancin mai shari'a O. Joel Omajali, ya bada umarnin tsare wanda ake zargin a hannun jami'an tsaro na farin kaya.

Wanda ake zargin dan asalin Ayingba ne a karamar hukumar Dekina ta jihar. An kama shi da laifin yada labaran bogi wanda zai iya tada hankulan jama'a.

A ranar Juma'a, ya ki amsa laifinsa a kan zargin da ake masa wanda ya aikata ranar 10 ga watan Yunin 2020.

Wanda ake zargin ya tada hankalin jama'a da karyarsa inda yace jama'a na rasuwa saboda zazzabi mai alaka da cutar korona a jihar, akasin matsayar gwamnatin jihar a kan lamarin.

Labarin bogi: Kotu ta bai wa DSS umarnin ci gaba da tsare Matashi
Labarin bogi: Kotu ta bai wa DSS umarnin ci gaba da tsare Matashi. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zargin gwamnan arewa da Boko Haram: Wurin 'yan kasuwar kauye na samu labari - Mailafiya

Daraktan gurfanarwa na jihar Kogi, Habib Abdullahi, ya ce rashin amsa laifinsa zai zama babban kalubale ga binciken hukumar tsaron na farin kaya, don haka ba za a bada belinsa ba.

Deborah A. Olorunmaiye, lauyan wanda ke kare kansa, ta ce laifin ba wanda za a hana beli bane, kuma ta roki kotun da ta bada belin wanda ake zargin.

A hukuncinta, O. J. Omajali ta ce bayan sauraron kowanne fanni, ta bada umarnin ci gaba da tsare wanda ake zargin a hannun DSS har zuwa ranar 18 ga watan Augusta don duba bukatar belin.

A wani labari na daban, wata kotun Musulunci da ke zama a jihar Kano ta yanke wa wani tsoho hukuncin kisa ta hanyar jifa sakamakon laifin yi wa karamar yarinya fyade da aka kama shi da shi.

Mai shari'a Ibrahim Sarki Yola, alkalin kotun, ya ce za a kashe tsohon mai suna Mati Audu ta hanyar jifa. Kotun ta samu Mati Audu mai shekaru 70 da laifin yi wa wata karamar yarinya mai shekaru 12 fyade a karamar hukumar Tsanyawa.

Tsoho Mati Audu ya tabbatar wa da kotun cewa shi ya aikata laifin fyaden. An dage shari'ar har sau hudu inda alkalin ya ba shi dama ko zai sauya ra'ayinsa da shaidarsa.

Amma kuma, a kowanne karo da aka koma zaman kotun, ya jaddada cewa shi ya yi wa karamar yarinyar fyade inda ya bukaci a yafe masa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel