Zargin gwamnan arewa da Boko Haram: Wurin 'yan kasuwar kauye na samu labari - Mailafiya

Zargin gwamnan arewa da Boko Haram: Wurin 'yan kasuwar kauye na samu labari - Mailafiya

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Dr. Obadiah Mailafiya, a ranar Alhamis ya ce ya samu bayanin cewa kwamandan Boko Haram gwamna ne a arewa daga bakin wasu 'yan kasuwa da ya hadu da su.

A yayin magana a kan tsokacinsa, Mailafiya, wanda ya zargi cewa wani gwamnan arewa ne kwamandan Boko Haram ya ce wasu 'yan kasuwa Fulani ne da ya zanta da su a wata kasuwar kauye suka sanar da shi.

Ya bada hakuri ga dukkan wadanda tsokacinsa ya bata wa rai, ya ce bai yi da niyyar bata wa kowa ba. Ya kara da cewa bai yi niyyar assasa rashin zaman lafiya ba.

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin, wanda ya zanta da wani gidan rediyo, ya zargi gwamnan da yunkurin assasa yakin basasa a Najeriya nan da 2022.

Gidan rediyon sun gayyacesa ne don yin jawabi a kan harin 'yan bindiga a arewa maso yamma da kuma rikicin kudancin Kaduna da ya tsananta.

Bayan wannan zargin, jami'an tsaron farin kaya na jihar Filato a ranar Alhamis sun gayyaci Mailafiya don amsa tambayoyi, inda ya kwashe tsawon sa'o'i bakwai kafin su sake shi.

Zargin gwamnan arewa da Boko Haram: Wurin 'yan kasuwar kauye na samu labari - Mailafiya
Zargin gwamnan arewa da Boko Haram: Wurin 'yan kasuwar kauye na samu labari - Mailafiya. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan sanda sun cafke 'yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane 27

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin ya ce ya yi magana ne saboda kishin arewa da kasar baki daya, amma bai san cewa bidiyon zai yadu ba.

A wata tattaunawa da Mailafiya yayi da BBC Hausa, Mailafiya ya ce ya amince har yayi hira da mutanen da bai sani ba kuma bai san cewa suna nada ba.

"A zatona gidan rediyo ne kadai a Legas," yace.

Ya ce duk da bai so tsokacinsa ya yadu ba, ba zai iya karyata yin su ba saboda shi masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne kuma saboda arewa da Najeriya ne yayi tsokacin.

Amma kuma, Kungiyar gwamnonin arewa a ranar Laraba ta yi kira ga cibiyoyin tsaro da su binciki zargin da tsohon mataimakin shugaban bankin Najeriya, Dr. Obadiah Mailafiya, na cewa "daya daga cikin gwamnonin arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya".

A wata takarda da aka fitar a garin Jos, Dr. Mukut Simon Macham, daraktan yada labarai da sadarwa na shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya ce kungiyar gwamnonin arewa ta matukar damuwa da wannan zargi mai girma na Mailafiya, wanda dole ne a bincika da gaggawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel