Malaman addinai ne suke assasa wutar rikicin Kudancin Kaduna - El-Rufai

Malaman addinai ne suke assasa wutar rikicin Kudancin Kaduna - El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a ranar Alhamis ya zargi wasu malaman addini sa zama musabbabin rikici a jihar.

El-Rufai, wanda ya zanta da shugaban cocin Anglika ta Najeriya, Rabaren Henry Ndukuba, wanda ya shugabanci wakilai wurin ziyartar gwamnan a gidan gwamnatin, ya ce "manyan masu assasa rikici sune wasu malamai da ke amfani da damar da suka samu wurin hada fitina a maimakon addini. Suna raba kan al'umma tare da assasa rikici."

Tun farko, Babban Rabaren Ndukuba ya ce "Na yarda cewa idan kiristoci da Musulmi za su tsaya a kan koyarwar addinansu, ba za su taba tada fitina ba kuma kasar nan za ta ci gaba."

Kungiyar manyan malaman addinin kirista na arewa, ta yi kira ga gwamnati da ta gaggauta bai wa yankin kudancin Kaduna tsaron da ya dace.

Shugaban kungiyar, JohnPraise Daniel, ya sanar da manema labarai hakan a garin Abuja a ranar Talata. Ya ce dole ne a kawo karshen kashe-kashen da ake yi a kudancin Kaduna da gaggawa.

Daniel, wanda shine ya kirkiro cocin Dominion ta duniya, ya ce dole ne gwamnati ta tabbatar da an damke wadanda ke aika-aikar da kuma masu daukar nauyinsu.

Malaman addinai ne suke assasa wutar rikicin Kudancin Kaduna - El-Rufai
Malaman addinai ne suke assasa wutar rikicin Kudancin Kaduna - El-Rufai. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Obaseki ya sha da kyar, an ba shi sarauta a karamar hukumar Oshiomhole

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ta ce ta damke mutum 27 da ake zargi da laifin fashi da makami da kuma garkuwa da mutane a jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Bola Longe, ya sanar da manema a garin Lafia a ranar Litinin, cewa wadanda ake zargin an kama su ne a sassa daban-daban na jihar cikin makonni biyu.

A yayin kama wadanda ake zargin, Longe, a hedkwatar 'yan sanda da ke Lafia, ya ce daga cikinsu akwai wadanda ke da alaka da kisan dagacin kauyen Odu da ke karamar hukumar Nasarawa, Amos Obere, a ranar 31 ga watan Yuli.

Ya yi bayanin cewa, wadanda ake zarginsu da kisan dagacin an kama su ne a wata mashaya da ke birnin Nassarawa inda suke shagalinsu.

Ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifinsu na garkuwa da mutane a kauyen Loko, wadanda ke kan hanyar zuwa Otukpo a jihar Binuwai daga Abuja, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel