Zaben Edo: INEC za ta dauki ma'aikata 20,000 na wucin-gadi

Zaben Edo: INEC za ta dauki ma'aikata 20,000 na wucin-gadi

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, ta ce za ta dauki ma'aikatan wucin-gadi 20,000 saboda zaben gwamnan jihar Edo da za a gudanar a ranar 19 ga watan Satumba.

Bolade Eyinla, jami'in hukumar INEC, shi ne ya labarta hakan a ranar Alhamis kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Eyinla, mashawarci kan harkokin gudanarwa ga shugaban hukumar na kasa, Mahmoud Yakubu, shi ne ya sanar da hakan a wani shirin sanin makamar aiki da horaswa da manema labarai da aka gudanar a brinin Benin.

Ya ce hukumar na bukatar wannan adadi na ma'aikata domin zaben gwamnan jihar da za a gudanar a rumfunan zabe 2, 627 cikin dukkan unguwanni 192 na jihar.

Shugaban Hukumar INEC na kasa; Farfesa Mahmoud Yakubu
Shugaban Hukumar INEC na kasa; Farfesa Mahmoud Yakubu
Asali: UGC

Ya kuma sanar da cewa, a yayin da ake daf da kammala duk wani shiri, hukumar ta tanadi dukkanin kayayyakin zaben da za a ribata yayin gudanar da zaben.

Ya sanar da cewa, a halin yanzu adadin masu rajistar zabe a jihar sun kai 2, 210,534, yayin da mutum 1,735,910 suka karbi katin su na zabe, sai kuma mutum 483,868 da har yanzu suna nan a hannun hukumar.

KARANTA KUMA: Adadin masu cutar korona a Najeriya ya zarta 47,000 - NCDC

Mista Eyinla ya yi bayanin cewa, jam'iyyun siyasa 14 ne suka gabatar da 'yan takara da za su fafata a zaben gwamnan da za a gudanar a watan gobe.

Ya ce a yayin da duk 'yan takara na jam'iyyu 12 suka kasance maza, 'yan takara na ragowar jam'iyyun biyu sun kasance mata.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Hukumar Zabe ta Kasa mai zaman kanta INEC, ta bayyana cewa a ranar 31 ga Oktoba ne za a gudanar da zabukan cike gurbi na mazabu guda 12 wadanda suka rage a dukkan fadin kasar.

Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa wadda Babban Kwamishina kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe na hukumar, Mista Festus Okoye, ya bayar a Abuja ranar Talata.

Mista Okoye ya ce ba don annobar korona da ake fama da ita, da tuni hukumar ta gudanar da zabubbukan.

Zabubbukan cike gurbin da su ka rage su ne na Yankin Tsakiya na Mazabar Sanata a Jihar Bayelsa; Mazabar Yamma ta Sanata a Bayelsa; Mazaɓun Nganzai da Bayo a Jihar Borno; Mazabar Arewa ta Sanata a Jihar Kuros Riba; da Mazaɓar Obudu a Kuros Riba.

Sauran su ne Mazaɓar Arewa ta Sanata a Jihar Imo; Mazabar Gabas ta Sanata a Jihar Legas; Mazabar Kosofe II a Jihar Legas; Mazabar Kudu ta Sanata a Jihar Filato; Mazaɓar Bakura a Jihar Zamfara, da Mazabar Ibaji a Jihar Kogi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng