Sai duhun dare ya kawo Mata ke zuwa karbar maganin tsarin iyali a Bauchi - Bincike

Sai duhun dare ya kawo Mata ke zuwa karbar maganin tsarin iyali a Bauchi - Bincike

A wani rahoto da jaridar Premium ta Times ta ruwaito, an gano babban dalilin da ya sa Matan aure ke fita cikin dare wajen neman maganin tsarin iyali da tazarar haihuwa a Bauchi.

Wasu matan aure a jihar Bauchi na fita neman maganin tsarin iyali da tazarar haihuwa yayin da duhun dare ya kawo ba tare da mazajensu sun sani ba.

Aisha Abdulkarim, jami’ar kula da tsarin iyali da tazarar haihuwa a jihar, ita ce ta sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai na kamfanin dillancin labarai na kasa a ranar Alhamis.

Matan Aure
Hoto daga jaridar Daily Nigerian
Matan Aure Hoto daga jaridar Daily Nigerian
Asali: Twitter

Ta ce galibin matan aure da ba su samu hadin kai daga wurin mazajensu ba, su kan sulale yayin da hasken rana ya dauke wajen fita neman maganin tsarin iyali da tazarar haihuwa.

Sai dai ta ce akan kuma samu wasu mazajen da su da kansu suke rako matansu wajen karbar maganin na tsarin iyali da tazarar haihuwa.

Aisha yayin zantawa da manema labarai a karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi, ta ce ana samun akalla matan aure 100 da ke zuwa karbar maganin tsarin iyali da tazarar haihuwa duk wata a kananan cibiyoyin lafiya 72 da ke jihar.

KARANTA KUMA: Wahalar samun wurin binne mutane ta tayar da hankalin al'umma a Kano

Ta ce mafi akasarin matan da ke fuskantar matsaloli da mazajensu ta hana su shan maganin tsarin iyali, su kan kai ziyara cibiyoyin lafiyar a tsakanin karfe 7.00 zuwa 8.00 na dare yayin da duhu ya kawo jiki.

Dalilinsu kamar yadda ta zayyana, ta ce a wannan lokaci matan sun tabbatar mazajen su na wuri guda. Haka kuma su kansu matan sun fi samun sukunin fita a wannan lokaci da babu abin da zai dauke musu hankali.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel