An daure sojan Najeriya da ya kashe ma'aikacin Hukumar Lafiya ta Duniya

An daure sojan Najeriya da ya kashe ma'aikacin Hukumar Lafiya ta Duniya

Wata kotun dakarun tsaro da ke zamanta a garin Abuja, ta zartar da hukuncin cin sarka na shekaru 55 a gidan kaso kan wani soja da aka tabbatar masa da laifin kisan kai da fashi da makami.

Sojan, Kofura Ibrahim Babangida, an zarge shi da laifin kashe wani Bello Aliyu bayan ya yi masa fashi da makamin motarsa a karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara tun a shekarar 2014.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, Marigayi Bello yayin rayuwarsa ya kasance ma’aikacin Hukumar Lafiya ta Duniya WHO a jihar.

Haka kuma an zargi Kofura Ibrahim da laifin satar wayar salula da kuma naira dubu dari shida daga mutane da dama a lokuta mabanbanta.

Sojojin Najeriya
Hoto daga jaridar Guardian
Sojojin Najeriya Hoto daga jaridar Guardian
Asali: UGC

Shugaban kotun, Manjo Janar Priye Fakrogha, yayin zartar da hukunci bayan sauraron hujjojin lauyoyi, ya ce Sojan da ake tuhuma zai ci sarka ta tsawon shekaru 40 a gidan dan Kande.

Sai dai an tattaro cewa, wannan hukunci zai biyo ta hannun Hukumar da ke sa ido kan dakarun sojin kasa gabanin a tabbatar da shi.

A wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi ya gudanar da wani taro da gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, dangane da matsalar tsaro da ta addabi jihar.

KARANTA KUMA: An kwaso 'yan Najeriya 386 da suka makale a ketare

Zulum, wanda ya yi tsokaci kan harin da ya tsallake ta baya baya tare da tawagarsa, ya jaddada bukatar daukar matakai na kawo karshen matsalar tsaro.

Shugaban kasar ya sha alwashin daukar matakan, wadanda za su iya hadawa da yin garanbawul ga shuwagabannin tsaro da ke a jihar Borno.

A cewar wata majiya, shugaba Muhammadu Buhari ya kadu kwarai da rahotannin da ya samu a hannun gwamnan kan kalubalen da Arewa maso Gabas ke fuskanta ta fuskar tsaro.

Wata majiyar ta ce: "Gwamnan ya ce babu abunda al'ummar jihar Borno ke bukata da ya wuce samar da tsaron rayuka da dukiyoyinsu, wanda ya gagara samuwa har yanzu.

Majiyar, da ta yi tsokaci kan yaki da Boko Haram a Borno, ta ce: "Babbar matsalar itace wasu manyan jami'an soji sun mayar da Baga wata cibiyar kasuwancinsu.

"Suna sana'ar sayar da kifi da tsuntsaye. A wannan sana'ar ne suke samun makudan kudaden da ake gani suna samu.

"Da yawa daga cikin wadannan jami'an sun saye tsuntsayen yanki baki daya.

Garin Baga na samar da kashi 45 na busasshen kifin da ake amfani da shi a Nigeria. Yana daya daga cikin garuruwa masu albarkar kasar noman tumatur da kayan lambu.

sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel