An kwaso 'yan Najeriya 386 da suka makale a ketare

An kwaso 'yan Najeriya 386 da suka makale a ketare

Kimanin ‘yan Najeriya 386 ne Gwamnati ta kwaso tare da dawo da su gida daga Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma kasar Lebanon.

Hakan na zuwa ne a yayin da Gwamnatin Najeriya ke ci gaba da fafutikar agazawa ‘yan kasarta da suka makale a ketare sakamakon takunkumin hana zirga-zirga da aka gindaya sanadiyar annobar korona.

Hukumar da ke kula da ‘yan Najeriya mazauna ketare (NIDCOM), cikin wani sako da ta wallafa ranar Laraba kan shafinta na Twitter, ta ce an kwaso ‘yan Najeriya 292 daga Hadaddiyar Daular Larabawa.

An kwaso 'yan Najeriya 386 da suka makale a ketare
Hoto daga hukuma NIDCOM
An kwaso 'yan Najeriya 386 da suka makale a ketare Hoto daga hukuma NIDCOM
Asali: Twitter

An kwaso 'yan Najeriya 386 da suka makale a ketare
Hoto daga hukuma NIDCOM
An kwaso 'yan Najeriya 386 da suka makale a ketare Hoto daga hukuma NIDCOM
Asali: Twitter

An kwaso 'yan Najeriya 386 da suka makale a ketare
Hoto daga hukumar NIDCOM
An kwaso 'yan Najeriya 386 da suka makale a ketare Hoto daga hukumar NIDCOM
Asali: Twitter

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, a yanzu adadin ‘yan Najeriya da aka kwaso daga kasashen Larabawa ya kai 2,933 tun bayan fara aikin dawo da ‘yan kasar da suka makale a watan Yuni.

A sanarwar da Hukumar NIDCOM ta fitar, jirgin Emirates wanda ya yi dakon ‘yan Najeriyar da aka kwaso ya sauka filin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikwe da ke birnin Abuja da misalin karfe 2.30 na rana.

Haka kuma gwamnatin Najeriya ta dawo da ‘yan mata 94 daga kasar Lebanon wadanda aka yi safarar su zuwa kasar.

Gwamnatin ta yi wannan agaji bayan wani faifan bidiyo da ya karade yanar gizo wanda ya nuna ‘yan mata su na neman gwamnati ta taimaka ta maido su gida.

‘Yan matan sun sauka a filin jirgin saman kasa-da-kasa na Murtala Muhammad da ke birnin Ikko.

Hukumar NIDCOM ta sanar cewa an dawo da 94 daga cikin ‘yan Mata 150 da suka makale a kasar Lebanon a ranar Laraba, 12 ga watan Agustan 2020.

KARANTA KUMA: Yadda 'yan daban daji suka kashe abokina a harin da suka kai jihar Taraba - Silas

Hukumar ta sanar cewa a yayin da sakamakon gwaji ya tabbatar dukkan wadanda aka dawo da su ba sa dauke da kwayoyin cutar korona, haka kuma dole ne su killace kawunansa na tsawon makonni biyu kamar yadda ka’idodin gwamnati suka shar’anta.

Yayin tarbar ‘yan matan a filin jirgin sama, shugabar hukumar NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa, ta yaba wa dukkan wadanda suka yi ruwa da tsaki wajen samun nasarar dawo da ‘yan matan gida.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel