Zaben Nasarawa: Yadda masu zabe suka dinga sayar da kuri'a a kan N500 - YIAGA ta fasa kwai

Zaben Nasarawa: Yadda masu zabe suka dinga sayar da kuri'a a kan N500 - YIAGA ta fasa kwai

- YIAGA Africa, ta yi ikirarin cewa zaben cike gurbin kujerar Nasarawa ta tsakiya a majalisar wakilai na cike da magudi da sayen kuri'u

- Duk da an samu karancin masu zabe, matsalolin na'urar zabe, da rashin kiyaye dokokin lafiya, an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali

- Kari da sayen kuri'u, jam'iyyu sun samar da takunkumin fuska da ruwa da sabulun wanke hannudon yaudarar jama'a su zabi jam'iyyarsu

Wata kungiya mai zaman kanta, YIAGA Africa, ta yi ikirarin cewa zaben cike gurbin kujerar Nasarawa ta tsakiya a majalisar wakilai na cike da magudi da sayen kuri'u.

A ranar Asabar, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar da zaben cike gurbin a rumfunan zaben44 da ke a mazabar, bayan mutuwar wakilin mazabar Suleiman Adamu.

Adamu ya rasu ne a cikin watan Mayu sakamakon kamuwa da annobar COVID-19.

A cikin wata sanarwa a ranar Laraba, Samson Itodo, babban daraktan YIAGA Africa, ya ce jami'an sa ido na kungiyar sun bada rahoton yadda masu zabe ke sayar da kuri'a a kan N500.

"Duk da an samu karancin masu zabe, matsalolin na'urar zabe, da rashin kiyaye dokokin lafiya, an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali. Jami'an tsaro sunyi kokari sosai," a cewarsa.

"Masu zabe a karamar hukumar Nasarawa sun cancanci yabo na tsayawa a layi domin kad'a kuri'unsu duk da matsalar latti da aka samu kafin a fara zaben, ga kuma barazanar COVID-19.

KARANTA WANNAN: Yadda manyan jami'an soji suka watsar da yaki suka koma kiwon kifi da tsuntsaye a Borno

Zaben Nasarawa: Yadda masu zabe suka dinga sayar da kuri'a a kan N500 - YIAGA ta fasa kwai
Zaben Nasarawa: Yadda masu zabe suka dinga sayar da kuri'a a kan N500 - YIAGA ta fasa kwai
Asali: Twitter

"Hukumar INEC ta dauki matakan kariya daga COVID-19, kamar samar da takunkumin fuska, safar hannu, na'urar gwajin zafin jiki da kuma sinadarin kashe kwayoyin cuta a rumfunan zabe.

"Sai dai hukumar ta fuskanci kalubale na bada tazara tsakanin masu zabe da kuma tabbatar da masu zabe sun sanya takunkumin fuska a rumfunan zaben.

"Kari da sayen kuri'u, jam'iyyu sun samar da takunkumin fuska da ruwa da sabulun wanke hannu a rumfunan zabe duk don yaudarar jama'a su zabi jam'iyyarsu.

"Da wannan ya zama wajibi INEC da hukumomin lafiya su dauki darasi daga wannan zaben, wajen tabbatar da bin matakan kariya daga COVID-19 a zabukan jihar Edo da Ondo.

"Jam'iyyun siyasa, 'yan takara, da 'yan siyasa har yanzu na sayen kuri'u a bainar jama'a, kuma a gaban jami'an tsaro.

"Da yawan masu zaben suna sayar da kuri'arsu akan kudin da bai wuce N500 ko N1,000 ba, a mafi akasarin rumfunan zaben, musamman rumfuna masu lamba PU 004, UNG Mallam, PU 005, da kuma PU 006 Angwan Dutse."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel