Yadda manyan jami'an soji suka watsar da yaki suka koma kiwon kifi da tsuntsaye a Borno

Yadda manyan jami'an soji suka watsar da yaki suka koma kiwon kifi da tsuntsaye a Borno

- Majiya mai tushe ta tabbatar da yadda wasu manyan jami'an soji suka watsar da yaki, suka koma sana'ar kifi da tsuntsaye a Baga, jihar Borno

- Majiyar ta shaida cewa da jami'an sojin basu shiga harkar kifi da tsuntsaye ba, da cikin watanni shida zasu iya kawo karshen Boko Haram

- A ranar Lahadin da ta gabata ne gwamna Babagana Umara Zulum ya gana da shugaban kasa Buhari kan matsalar tsaro da ta addabi jiharsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi ya gudanar da wani taro da gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, dangane da matsalar tsaro da ta addabi jihar.

Zulum, wanda ya yi tsokaci kan harin da ya tsallake ta baya baya tare da tawagarsa, ya jaddada bukatar daukar matakai na kawo karshen matsalar tsaro.

Shugaban kasar ya sha alwashin daukar matakan, wadanda za su iya hadawa da yin garanbawul ga shuwagabannin tsaro da ke a jihar Borno, a cewar jaridar The Nation.

A cewar wata majiya, shugaba Muhammadu Buhari ya kadu kwarai da rahotannin da ya samu a hannun gwamnan kan kalubalane da Arewa maso Gabas ke fuskanta ta fuskar tsaro.

Wata majiyar ta ce: "Gwamnan ya ce babu abunda al'ummar jihar Borno ke bukata da ya wuce samar da tsaron rayuka da dukiyoyinsu, wanda ya gagara samuwa har yanzu.

"Ya ce al'ummarsa har sun fara cire tsammani kan cewar za a kawo karshen Boko Haram, la'akari da yadda ake yiwa lamarin rikon sakainar kashi."

KARANTA WANNAN: Ku sanar dani yadda 'yan ta'adda ke samun makamai - Buhari ga hafsoshin tsaro

Yadda manyan jami'an soji suka watsar da yaki suka koma kiwon kifi da tsuntsaye a Borno
Yadda manyan jami'an soji suka watsar da yaki suka koma kiwon kifi da tsuntsaye a Borno
Asali: UGC

Majiyar, da ta yi tsokaci kan yaki da Boko Haram a Borno, ta ce: "Babbar matsalar itace wasu manyan jami'an soji sun mayar da Baga wata cibiyar kasuwancinsu.

"Suna sana'ar sayar da kifi da tsuntsaye. A wannan sana'ar ne suke samun makudan kudaden da ake gani suna samu.

"Garin Baga na samar da kashi 45 na busasshen kifin da ake amfani da shi a Nigeria. Tana daya daga cikin garuruwa masu albarkar kasar noman tumatur da kayan lambu a kasar.

"Da yawa daga cikin wadannan jami'an sun saye tsuntsayen yanki baki daya.

"Daura da barikin soji na Baga a yanzu ya zama wata babbar gona, mallakin wani babban jami'in soji."

Majiya mai tushen ta ce: "Mun samu tabbaci na shugaban kasa kan daukar mataki akan hakan, ya zama dole shugaban kasar ya dakatar da jami'an sojin daga watsar da lamuran jama'a akan bukatunsu.

"Idan aka kwatanta nasarar da dakarun soji suka samu a shekarun baya, tabbas da ace basu shiga kasuwancin kifi ba, to da ba zai daukesu watanni shida ba sun gama da ta'addancin mayakan Boko Haram."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel