Ku sanar dani yadda 'yan ta'adda ke samun makamai - Buhari ga hafsoshin tsaro

Ku sanar dani yadda 'yan ta'adda ke samun makamai - Buhari ga hafsoshin tsaro

- Shugaba Muhammadu Buhari ya tuhumi shuwagabannin tsaro kan yadda 'yan ta'adda ke samun makamai duk da cewa ya rufe bodar kasar

- Buhari ya hakikance cewa talauci da rashin aikin yi ne musabbabin matsalolin tsaro a kasar

- Sai dai shugaban kasar ya karyata jita jitar cewa 'yan ta'addan Arewa maso Gabas sun fi gwamnati kudi da makamai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tuhumi shuwagabannin hukumomi da rundunonin tsaro kan yadda 'yan ta'adda ke samun makamai duk da cewa ya rufe bodar kasar.

Da yake jawabi a taron gwamnonin jihohi da shuwagabannin tsaro a ranar Talata a Abuja, ya nuna damuwarsa kan yadda 'yan ta'addan ke samun makaman da suke ta'addanci a kasar.

"Wadannan 'yan ta'addan suna rayuwa a cikin kauyuka. Amma me yasa makamansu basa karewa?" ya tuhumi shuwagabannin hukumomin tsaro da hafsoshin rundunar soji.

Taron ya kare da yin kira kan samar da dabaru na kawo karshen ta'addanci farat daya, yayin da jami'an tsaro zasu mayar da hankali wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Taron ya mayar da hankali kan matsalolin tsaro da yadda za a shawo kansu, inda aka nuna muhimmancin killace bayanan sirri domin karya lagon 'yan ta'addan.

Mahalarta taron sun nuna yakininsu na cewar idan aka sake samun yarda tsakanin jami'an tsaro da mutanen gari, to za a samu nasara wajen tattara bayanan sirri mai yawa kan 'yan ta'addan.

KARANTA WANNAN: Buhari ya shiga ganawa da gwamnonin Arewa maso Gabas da hafsoshin tsaro

Ku sanar dani yadda 'yan ta'adda ke samun makamai - Buhari ga hafsoshin tsaro
Ku sanar dani yadda 'yan ta'adda ke samun makamai - Buhari ga hafsoshin tsaro
Asali: Facebook

A cewar wata sanarwa daga Garba Shehu, babban hadimin shugaban kasa ta fuskar watsa labarai, an hakikance cewa talauci da rashin aikin yi ne musabbabin matsalolin tsaro a kasar.

Shugaban kasar ya yi amfani da wannan damar wajen karyata jita jitar cewa 'yan ta'addan Arewa maso Gabas sun fi gwamnati kudi da makamai, yana mai cewa "yanzu 'yan ta'addan sun dawo fasa shaguna da kasuwanni, kashe farar hula don samun abincin da zasu ci."

Shugaba Buhari ya jaddada kiransa ga shuwagabannin tsaro dasu zage damtse yana mai cewa dole su hada kansu don kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi kowa a kasar.

A ranar Litinin kuwa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnoni shida na jihohin Arewa maso Gabas.

A cewar wakilin gidan talabijin Channels TV, gaba daya hafsoshin tsaro tare da sifeta janar na rundunar 'yan sanda na cikin mahalarta taron.

Taron na gudana ne bayan da gwamnonin a makon da ya wuce suka zabi gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin shiyyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel