Gwamna Lalung ya bayyana damuwa kan yadda ta'ammali da miyagun kwayoyi ya yi kamari a Filato

Gwamna Lalung ya bayyana damuwa kan yadda ta'ammali da miyagun kwayoyi ya yi kamari a Filato

Gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya bayyana damuwa kwarai dangane da yadda ta’ammali da miyagun kwayoyi ke ci gaba da tsananta a jiharsa.

Gwamnan ya bayyana damuwa matuka kan yadda lamarin ke kara ta’azzara duk da kokarin da masu ruwa da tsaki ke ci gaba da yi domin kawo karshen wannan mummunar ta’ada.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito Lalung yana cewa, gwamnatinsa ba za ta lamunce da duk wani hargitsi a zaman lafiya na jihar ba a kowane irin tasiri na maye.

A yayin da hukumar NDLEA mai yaki da ta’ammali da fataucin miyagun kwayoyi ta kone tarin kayan maye masu yawan gaske, Lalung ya lura cewa tabbas wannan fasadi ya munana a jiharsa.

Yayin da hukumar NDLEA ta kone miyagun kwayoyi
Yayin da hukumar NDLEA ta kone miyagun kwayoyi
Asali: Twitter

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin kone tulin miyagun kwayoyin a bainar jama’a da aka gudanar a Dutsen Nanfang da ke Unguwar Du ta karamara hukumar Jos ta Kudu.

Lalung ya ce a zahiri wannan lamari ya nuna irin babban hatsarin ta’ammali da fataucin miyagun kwayoyi da ake fuskanta a jihar.

Gwamnan ya ci gaba da bayyana damuwa a yayin da hukumar NDLEA ta tarwatsa miyagun kwayoyin, lamarin da ya ce duk da irin kokarin sa gwamnati ta ke yin a magance wannan musiba amma har yanzu haka bata cimma ruwa ba.

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar NDLEA ta kone tulin kayen maye wanda nauyinsu ya kai kilo 16.697 da aka kwato a hannun masu safarar miyagun kwayoyi a jihar.

A yayin da tuni an zartar da hukuncin kan wasu daga cikin masu aikata irin wannan mummunan fasadi, wasu ko ana ci gaba da bincike da gudanar da shari’a a kansu.

KARANTA KUMA: A koda yaushe zan kasance mai goyon bayan matasa - Atiku

A dalilin haka ne Gwamnan yake neman hadin kan shugabannin addinai, sarakunan gargajiya da kuma kungiyoyi masu zaman kansu domin agazawa kokarin da gwamnati ke yi na magance wannan musiba.

Haka kuma gwamnan ya umarci kwamishinan Ilimi na manyan makarantu da ya bijiro da wani sabon tsari na wayar da kan dalibai a kan illolin dake tattare da ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Ya ce ya zama wajibi gwamnatinsa ta bullo da wasu sabbin matakai da kuma dabarun tseratar da al’umma musamman matasa daga gurbata rayuwarsu da miyagun kwayoyi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel