Gwarzo: Wani matashi ya aura mata biyu a lokaci daya kuma rana daya (Hotuna)

Gwarzo: Wani matashi ya aura mata biyu a lokaci daya kuma rana daya (Hotuna)

- Wani matashi dan asalin kasar Kamaru ya tada hankalin samari da 'yan mata a kafafen sada zumuntar zamani

- Kamar yadda hotunan da suka bayyana suka nuna, matashin ya aura zuka-zaukan mata har biyu a rana daya

- A hotunan, an ga amarensa biyun cike da annashuwa da farin ciki na auren rabin ransu da suka yi

Wani mutum dan asalin kasar Kamaru ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani a kan auren da yayi.

Bawan Allan ya aure mata zuka-zuka har biyu a rana daya, kuma a coci daya aka yi daurin auren, jaridar The Nation ta wallafa.

A hotunan bikin, an ga angon bakinsa har kunne inda yake matukar farin ciki yayin da suke daukar hoto.

Hotunan sun bazu a kafafen sada zumunta kuma sun tada hankalin samari da 'yan mata. Wasu samarin na fatan 'Allah kai damo ga harawa', yayin da wasu ke ganin ba za su iya ba.

Hakazalika, a hotunan bikin da suka bazu, an ga matan cike da farin ciki tare da annashuwa a kan auren rabin ransu da suka yi.

Ga hotunan bikin:

Gwarzo: Wani matashi ya aura mata biyu a lokaci daya kuma rana daya (Hotuna)
Gwarzo: Wani matashi ya aura mata biyu a lokaci daya kuma rana daya (Hotuna). Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel