Gwamna Matawalle ya ba da umarnin biyan N50,000 ga Dagatai duk wata

Gwamna Matawalle ya ba da umarnin biyan N50,000 ga Dagatai duk wata

Gwamna Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya umarci dukkan shugabannin kananan hukumomi 14 da su fara biyan alawus na N50,000 duk wata ga kowane dagaci a kananan hukumominsu.

Gwamnan ya sanar da hakan ne ta bakin hadiminsa na musamman kan harkokin sadarwa, Zailani Bappa kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Zailani ya ce Gwamnan ya ba da wannan umarni yayin da kungiyar dagatai ta jihar ta kai masa ziyara har fada a ranar Talata, 11 ga watan Agusta.

Kazalika gwamnan ya kuma ba da kyautar motoci uku ga kungiyar dagatan, wadda kowace daya daga cikin shiyoyi na mazabu uku da jihar ta kunsa za su ci moriya.

Yayin yi wa gwamnan godiya dangane da wannan karamci, kungiyar ta ce ta ziyarci fadar gwamnan domin jaddada goyon bayanta a kan gwamnatinsa.

Gwamna Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara
Gwamna Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara
Asali: UGC

Kungiyar ta ce za ta ci gaba da goyon bayan Gwamna Matawalle domin cimma manufar samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.

A nasa jawaban, Gwamna Matawalle ya nemi dagatai da su yi amfani da rawaninsu wajen rikon amana ta biyan bukata da kuma hidimtawa al’ummominsu.

Ya ce rawar da za su taka kasancewarsu sarakunan gargajiya, it ace nesanta kansu daga shiga ko kuma nuna bangaranci a harkokin siyasa.

Ya gargade su a kan goyon bayan da tallafawa gwamnati domin tabbatar da ci gaban jihar da al’umma baki daya.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a ranar Litinin, 10 ga watan Agusta, Gwamna Matawalle, ya rantsar da sabbin mashawarta 15 na musamman da ya dora wa nauyin taya shi riko da akalar jagoranci.

Yayin rantsuwar da aka gudanar cikin birnin Gusau, Gwamnan ya bayyana cewa wannan nadin mukamai na daga cikin al’adar da aka saba don inganta harkokin gudanarwa da zai tallafi gwamnati wajen sauke nauyin al’umma.

Ba ya ga taya su murnar samun wannan mukamai, Gwamnan ya kuma yi gargadi a kan kada su bari bukatunsu na karan-kai su yi tasiri yayin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

“An nada ku ne domin yi wa jihar hidima bisa la’akari da kwazon aiki da kuka nuna a baya wajen jajircewa da sadaukar da kai a kan samar da ci gaba mai dorewa a jihar.”

“Saboda haka ina da yakinin cewa ba za ku bani kunya ba wajen bayar da himma da kara kaimi doriya a kan wadda kuka yi a baya.”

KARANTA KUMA: Muna roƙon 'yan Najeriya su ƙara haƙuri kan matsalar rashin tsaro - Buhari

“A yayin da a yanzu din nan aka rantsar da ku, ina so nayi amfani da wannan daman a tunatar da ku nauyin da ke kanku, wanda bai wuce tabbatar da rikon amanar da gwamnati ta danka a hannun ku ba.”

“Ana tsammanin za ku ribaci kwarewar da kuke da ita wajen sauke nauyin da aka rataya muku tare da daura damarar kawo managarcin sauyi a koda yaushe.”

“Gaskiya da adalci su ne kyawawan dabi’u da suka wajaba ku yi riko da su yayin sauke nauyin da ya rataya a wuyanku.”

A karshe Gwamnan ya kirayi al’ummar jihar da su bai wa sabbin hadiman goyon bayan na hakiki da zai yi tasiri wajen basu damar sauke nauyin da ke kansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel