Dakarun Nijar sun harbe masu kai wa 'yan Boko Haram makamai a kan hanyarsu ta zuwa Najeriya

Dakarun Nijar sun harbe masu kai wa 'yan Boko Haram makamai a kan hanyarsu ta zuwa Najeriya

- An kashe mutum hudu ‘yan kasar Libiya da ake zargi sun taho da dakon makamai na mayakan Boko Haram

- Dakarun sojin kasar Nijar ne suka datse mu hanya a kan iyakar Najeriya

- Tsawon fiye da shekaru goma da suka gabata, tayar da zaune tsayen da kungiyar Boko Haram ke ci gaba da yi ya hargitsa Arewa maso Gabashin Najeriya

Akalla mutum hudu da ake zargi masu yi wa mayakan Boko Haram dakon makamai sun yi gamo da ajali a hannun sojojin kasar Nijar.

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin kasar Nijar sun kashe wasu mutum hudu ‘yan kasar Libiya a kan hanyarsu ta zuwa Najeriya dauke da tarin makamai masu yawa.

Dakarun Nijar sun datse hanyar ‘yan ta’adda a ranar Lahadi a kan hanyarsu da zuwa Arewa maso Gabashin Najeriya.

Dakarun Nijar sun harbe masu kai wa 'yan Boko Haram makamai a kan hanyarsu ta zuwa Najeriya
Dakarun Nijar sun harbe masu kai wa 'yan Boko Haram makamai a kan hanyarsu ta zuwa Najeriya
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar The Guardian ta wallafa, Sojojin Nijar sun tare masu dakon makaman gabanin su isa iyakar Najeriya.

Babu shakka musibar ta’addancin kungiyar masu tayar a kaya baya ta Boko Haram ya zamto abin tsoro mai munin gaske ga mazauna yankin Arewa maso Gabas da kuma Arewa maso Yamma.

Tun bayan da kungiyar Boko Haram ta daura damarar ta’addanci a Najeriya shekaru fiye da goma da suka gabata, ta tarwatsa alkaryu ta hanyar kashe mutane bila adadin da dubban mutane tsuguno a mahallansu.

Haka kuma Legit.ng ta ruwaito cewa, a baya bayan nan ne gwamnatin Amurka ta ankarar da Najeriya a kan gargadin cewa ‘yan ta’adda Al Qa’eda sun fara shiga wasu jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya.

KARANTA KUMA: Covid-19: Kananan hukumomi 85 na jihohi 20 a tarayya suna nan ba tare da an yi gwaji ba - Boss Mustapha

A yayin da rashin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a Najeriya, Gwamnatin Birtaniya ta gargadi wasu ‘yan kasarta a kan tafiya zuwa wasu jihohin Najeriya.

Gargadin ya fito ne cikin wata sanarwa da Gwamnatin ta wallafa a kan shafinta na yanar gizo, inda ta ce babu aminci a wasu yankuna na Najeriya.

Daga cikin jihohin da Birtaniya ta gargadi al’ummarta a kan kai ziyara sun hadar da Borno, Yobe, Adamawa and Gombe, Kaduna, Kano, Bauchi, Niger, Jigawa, Katsina, Zamfara, da Kogi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel