Fashewar abubuwa a Buirut: Firam Ministan Lebanon da mukarrabansa sun yi murabus

Fashewar abubuwa a Buirut: Firam Ministan Lebanon da mukarrabansa sun yi murabus

Gwamnatin kasar Lebanon karkashin Firam Minista Hassan Diab ta yi murabus, bayan da abubuwan fashewa suka tarwatsa babban birnin kasar a makon da ya gabata, inda akalla mutane 200 suka mutu, yayin da 6,000 suka jikkata.

Shugaban kasar Michel Aoun ya amince da murabus din Diab a ranar Litinin, inda ya bukaci ta yi shugabancin rikon kwarya har zuwa lokacin da za a yi zaben sabbin shuwagabanni.

Hankula na ci gaba da tashi a kasar tun bayan da wasu abubuwa suka fashe a tashar ruwa ta Beirut, da yayi sanadin mutuwar akalla mutane 200 da jikkata sama da mutane 6000.

"Wannan laifin" ya faru sakamakon cin hanci "da rashawa ya fi karfin kasar", a cewar Diab a jawabin kai tsaye, yana mai cewa, zai yi murabus ne don tsayawa tare da jama'arsa.

"A yau, zamu bi bukatar al'umarmu, na son hukunta wadanda suka yi sanadin fashewar wadannan abubuwa, da suka dade suna boyewa tsawon shekaru bakwai, da burinsu na son ayi canji," a cewarsa.

KARANTA WANNAN: FG za ta kashe N2.3trn wajen samar da hasken lantarki a kauyuka

Fashewar abubuwa a Buirut: Shugaban kasa Lebanon da mukarrabansa sun yi murabus
Fashewar abubuwa a Buirut: Shugaban kasa Lebanon da mukarrabansa sun yi murabus
Asali: Twitter

"A yau na sanar da murabus din gwamnatina. Allah ya kare Lebanon," a cewar Diab, yana mai maimaita kalmar karshe har sau uku.

Murabus din ya zo ne bayan wata zanga zangar nuna fushi da al'umar kasar suka gudanar a karshen makon jiya, inda aka jikkata mutane 728 tare da kashe jami'in dan sanda.

Tsarin gwamnatin kasar ya yi nuni da cewa Aoun zai tuntubi majalisar tarayyar kasar akan wanda zai zama firam minista na gaba, dole ya samu karbuwa daga 'yan majalisar.

A ranar 4 ga watan Agusta ne, wani sinadarin ammonium nitrate mai nauyin tan 2,000 ya fashe, inda ya kashe akalla mutane 200, ya jikkata sama da mutane 6,000 tare da lalata birnin Buirut.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel