Ana iya yin jimami duk yadda aka ga dama idan na mutu - Obasanjo

Ana iya yin jimami duk yadda aka ga dama idan na mutu - Obasanjo

Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya mayar da martani dangane da irin salo na sakon ta’aziyar da ya rubuta kan mutuwar Sanata Buruji Kashamu, jigo na jam’iyyar PDP a jihar Ogun.

Obasanjo cikin sakon ta’aziyyar, ya ce marigayi Kashamu ya shallake duk wani hukuncin da kasar Amurka za ta zartar a kansa kan laifin fataucin miyagun kwayoyi dake tuhumarsa, amma bai iya tsere wa mutuwa ba.

“Sanata Esho Jinadu yayi duk wani shige da fice na ganin ya tsere wa fuskantar hukuncin laifukan da ake tuhumarsa a ciki da wajen Najeriya, amma babu wani tsimi ko dabara da ya iya hana mutuwa ta cimma sa.”

Tsohon Shugaban Kasa; Olusegun Obasanjo
Tsohon Shugaban Kasa; Olusegun Obasanjo
Asali: UGC

“Babu wata dabara ta siyasa, al’ada, magani ko shari’a da za ta iya hana mutuwa domin kuwa a hannun Mahallacin mu take, kuma da lokacin mutum ya yi dole sai ya amsa kira.

“Allah ya yafe masa kurakuransa kuma ya sanya Aljannah ce makoma sannan kuma ya bai wa iyalinsa da makusanta jiriya da hakurin wannan babban rashi da suka yi,” inji Obasanjo.

Sai dai ‘yan Najeriya da dama sun soki Obasanjo dangane da wannan sako na ta’aziya wanda suke ganin babu dattako a cikinsa.

Daga cikin masu mayar da martani akwai tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, wanda y ace bai dace ba a rika aibata wanda ya riga da ya mutu.

KARANTA KUMA: Jerin Sanatocin da suka fi kawo kudirorin samar da ci gaban kasa

Fayose ya ce “Obasanjo ya tuna cewa babu wanda ya san lokacin ballantana yanayin da ajali zai katsewa mutum hanzari.”

A cikin sakon da Fayose ya wallafa a kan shafinsa na Twitter, ya ce tsohon shugaban kasar bai tsarkaka daga aikata laifi ba saboda haka ya daina yi kansa kallo a matsayin wanda ba ya laifi.

Sai dai Obasanjo yayin mayar da martani a ranar Lahadi, ya ce mutane na damar yin jimamin wanda ya riga da ya mutu ta kowace irin salo da suka ga dama, amma kuma ya zama wajibi wanda ke raye ya dauki darasi a kan wadanda suka shude.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel