FG za ta kashe N2.3trn wajen samar da hasken lantarki a kauyuka

FG za ta kashe N2.3trn wajen samar da hasken lantarki a kauyuka

- Gwamnatin tarayya ta shirya samar da hasken lantarki a kauyukan Nigeria, karkashin shirin Solar Homes Systems (SHS)

- Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya ce gwamnati ta zata kashe N2.3trn wajen samar da cibiyoyin sarrafa hasken rana zuwa lantarkin

- Haka zalika shirin ESP zai samar da ayyuka a fannin noma, inda akalla mutane miliyan biyar zasu amfana, da kuma ayyuka ta fannin gidaje

Shirin gwamnatin tarayya na Solar Homes Systems (SHS), da ke karkashin tsarin ESP, zai kashe N2.3trn wajen samar da hasken lantarki a kauyukan Nigeria.

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan, yana mai cewa, shirin SHS zai samar da cibiyoyin sarrafa hasken rana zuwa wutar lantarki ga gidaje miliyan 5.

A cewarsa, idan aka samar da kananun cibiyoyin, hakan zai sa akalla mutane miliyan 25 su amfana da hasken lantarkin a kauyukan da ke fadin Nigeria.

Osinbajo, a taron tattauna tsare tsaren gwamnatin tarayya na 2020 a cibiyar kasuwanci da masana'antu ta Lagos (LCCI), ya ce gwamnati ta ware N2.3trn domin samar da hasken lantarkin.

Ya ce, "Muna da zummar fara aikin da wuri, duba da cewa, sanya cibiyar sarrafa hasken ranar zuwa lantarki a gidaje miliyan 5 ba karamin aiki bane, dole a fara da wuri."

KARANTA WANNAN: Yan bindiga sun kashe mutane 13 a Benue

FG za ta kashe N2.3trn wajen samar da hasken lantarki a kauyuka
FG za ta kashe N2.3trn wajen samar da hasken lantarki a kauyuka
Asali: Depositphotos

Ya kara da cewa shirin ESP ya hada da tallafawa kananu da matsakaitan 'yan kasuwa, wajen bunkasa sarrafa magungunan cikin gida da samar da kayan yaki da cutar COVID-19.

Shirin ESP zai samar da ayyuka a fannin noma, inda akalla mutane miliyan biyar zasu samu aiki. Haka zalika akwai ayyuka ta fannin gina gidaje.

Shugabar cibiyar LCCI, Mrs. Toki Mabogunje, ta ce alkaluman tattalin arziki na nan kusa, basu nuna wani abun farin ciki ba, amma ta na sa ran lamuran su war ware a nan gaba.

Mrs. Maboguje ta ce, "Sai dai, muna da yakinin cewa tattalin arzikin Nigeria zai farfado. Muna da albarkatun kasa da yawa, kasuwanci na da fadi kuma mutane sun dukufa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel