Yan bindiga sun kashe mutane 13 a Benue
- Yan bindiga sun kai hari jihar Benue, akalla mutane 13 sun rasa rayukansu, rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin
- Ana hasashen cewa, wani ne ya dauki hayar 'yan bindigar domin kai farmaki garin Edikwu saboda neman sarauta
- Tun 1994 ne ake rikicin sarautar Alegwu na garin, rikicin da ya jawo asarar rayuka masu yawa
Akalla mutane 13 ne na kauyen Edikwu, da ke cikin garin Ugbokpo, karamar hukumar Apa, jihar Benue ne suka rasa rayukansu a wani harin safiya da 'yan bindga suka kai masu.
Ana hasashen cewa, wani ne ya dauki hayar 'yan bindigar ne domin kai farmaki garin Edikwu saboda ya sha kasa a bada sarautar Alegwu (Sarkin) Edikwu.
Wakilin jaridar Leadership, ta hannun wasu 'yan garin ya tattara rahoton cewa tun 1994 ne ake rikicin sarautar Alegwu na garin, rikicin da ya jawo asarar rayuka masu yawa.
Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, DSP Catherine Anene wacce ta tabbatar da kashe mutanen ta bayyana cewa sama da 'yan bindiga 20 ne suka farmaki garin.
Sun kai farmakin ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar Litinin, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 13, da jikkata wasu da dama.
KARANTA WANNAN: JAMB ta sanar da ranar fara zana jarabawar Post-UTME

Asali: Facebook
Anene ta bayyana cewa tuni aka tura jami'an rundunar garin da lamarin ya faru; kuma an gano gawarwaki 13, yayin da ake ci gaba da bincike.
Shima da yake tabbatar da harin, Sarkin Edikwu, Chief Otokpa David Imoni wanda ya zanta da Leadership ya bayyana cewa zuwa yanzu 'yan bindigar sun kashe sama da mutane 30.
A cewarsa, akwai wani mutumin da ya ke haddasa rikicin, saboda yana son sarautar garin, kuma bai yarda da masu nada sarki ba, tun zamanin tsohon Sarki Chief Imoni Otokpa.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan harin yazo ne watanni 3 bayan da mataimakin gwamnan jihar, Mr. Benson Abounu ya yi zaman sulhu da masu ruwa da tsaki na garin.
Chief Otokpa David Imoni ya ce, wanda ke haddasa rikicin, ya samu goyon bayan wasu 'yan siyasa, kuma ya dade yana tura 'yan bindiga suna kai hari garin, da cewar lallai sai an bashi sarautar garin, duk da cewa lamarin na gaban kotu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng