Matawalle ya rantsar da sabbin mashawarta na musamman 15 a Zamfara

Matawalle ya rantsar da sabbin mashawarta na musamman 15 a Zamfara

A ranar Litinin, 10 ga watan Agusta, Gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle, ya rantsar da sabbin mashawarta 15 na musamman da ya dora wa nauyin taya shi riko da akalar jagoranci.

Yayin rantsuwar da aka gudanar cikin birnin Gusau, Gwamnan ya bayyana cewa wannan nadin mukamai na daga cikin al’adar da aka saba don inganta harkokin gudanarwa da zai tallafi gwamnati wajen sauke nauyin al’umma.

Ba ya ga taya su murnar samun wannan mukamai, Gwamnan ya kuma yi gargadi a kan kada su bari bukatunsu na karan-kai su yi tasiri yayin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

Gwamnan Zamfara; Muhammad Bello Matawalle
Gwamnan Zamfara; Muhammad Bello Matawalle
Asali: UGC

“An nada ku ne domin yi wa jihar hidima bisa la’akari da kwazon aiki da kuka nuna a baya wajen jajircewa da sadaukar da kai a kan samar da ci gaba mai dorewa a jihar.”

“Saboda haka ina da yakinin cewa ba za ku bani kunya ba wajen bayar da himma da kara kaimi doriya a kan wadda kuka yi a baya.”

“A yayin da a yanzu din nan aka rantsar da ku, ina so nayi amfani da wannan daman a tunatar da ku nauyin da ke kanku, wanda bai wuce tabbatar da rikon amanar da gwamnati ta danka a hannun ku ba.”

KARANTA KUMA: Sanatoci 10 da suka shafe shekara ba tare da gabatar da kudiri ko daya ba a majalisa

“Ana tsammanin za ku ribaci kwarewar da kuke da ita wajen sauke nauyin da aka rataya muku tare da daura damarar kawo managarcin sauyi a koda yaushe.”

“Gaskiya da adalci su ne kyawawan dabi’u da suka wajaba ku yi riko da su yayin sauke nauyin da ya rataya a wuyanku.”

A karshe Gwamnan ya kirayi al’ummar jihar da su bai wa sabbin hadiman goyon bayan na hakiki da zai yi tasiri wajen basu damar sauke nauyin da ke kansu.

Idan ba a manta ba kimanin watanni biyu da suka gabata ne Gwamna Matawalle ya yi nadi tare da rantsar da sabbin kantomomi na kananan hukumomi 14 da ke jihar Zamfara.

Gwamna Matawalle cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Zailana Bappa ya gabatar, ya ce an yi sabbin nade-naden kwana daya kacal da sauke shugabannin kananan hukumomin.

Majalisar dokokin jihar ce ta yanke shawarar sauke dukkan shugabannin kananan hukumomin jihar 14 sakamakon tabargazar kudi da wulakantar da kujera da suka yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel