JAMB ta sanar da ranar fara zana jarabawar Post-UTME

JAMB ta sanar da ranar fara zana jarabawar Post-UTME

- JAMB ta sanar da sauya ranar zana jarabawar Post-UTME daga 2 ga watan Agusta zuwa ranar 7 ga watan Satumba, 2020

- An sauya ranar ne domin baiwa daliban da zasu zana jarabawar WAEC damar zana jarabawar Post-UTME a wannan shekarar

- Ga manyan makarantun da ke son gudanar da gwajin jarabawar Post-UTME, to a yi a rukuni biyu — Satumba 7 zuwa Oktoba 4

Hukumar zana jarabawar shiga manyan makarantu JAMB ta sanar da ranar fara tantance daliban da zasu zana jarabawar sharar fagen shiga manyan makarantu, wato Post-UTME.

Hukumar ta sanya ranar 7 ga watan Satumba, 2020 ya zamo ranar fara tantance daliban da ke sha'awar shiga jami'o'i, kwalejojin kimiya da fasaha da kuma kwalejojijn ilimi.

JAMB ta kuma sanar da rike sakamakon daliban da suka jana jarabawar UTME a cibiyoyin gyara hali na Nigeria bisa zargin aikata laifukan jarabawa.

Magatakardan hukumar JAMB, Farfesa Ish-aq Oloyede, ya bayyana hakan bayan wani taron neman shawara da shuwagabannin manyan makarantu, da aka gudanar ta yanar gizo.

Rahotanni sun bayyana cewa mutane 488 ne suka halarci taron, ta yanar gizo, daga jihohi 36 da ke a fadin kasar.

A cewar Olouede, da farko an sanya ranar 2 ga watan Agusta ta zamo ranar tantancewar, amma daga baya aka sauya ranar.

KARANTA WANNAN: FG ta umurci ma'aikata da ke a mataki na 12 da 13 su koma bakin aiki

JAMB ta sanar da ranar fara tantance zana jarabawar Post-UTME
JAMB ta sanar da ranar fara tantance zana jarabawar Post-UTME
Asali: UGC

A cewarsa, an sauya ranar ne domin baiwa daliban da zasu zana jarabawar kammala makarantar sakandire WAEC, damar janar jarabawar Post-UTME a wannan shekarar.

Ya ce, "A halin yanzu kamar yadda kuka sani, za a fara zana jarabawar WAEC a ranar 17 ga watan Agusta, za a ci gaba da zana jarabawar har sai 7 ga watan Satumba.

"A hannu daya, a ranar 21 ga watan Satumba, za a fara zana jarabawar NABTEB, kuma za a kammala ranar 15 ga watan Oktoba, da zaran an gama za a fara jarabawar NECO daga 5 ga watan Nuwamba har zuwa 18 ga watan Nuwamba.

"Maimakon raba hankalin dalibai, gwanda mu daga ranar jarabawar shiga manyan makarantu. Saboda watakila dalibi na da jarabawar WAEC, NABTEB ko NECO a Sokoto, kuma yana da jarabawar Post-UTME a Ibadan, to wanne zabi yake da shi?

"Ga manyan makarantun da ke son gudanar da gwajin jarabawar Post-UTME, to kada ya kai 7 ga watan Satumba, kuma a yi a rukuni biyu — Satumba 7 zuwa Oktoba 4.

"Kuma za a sake gudanar da jarabawar karo na biyu a ranar 18 ga watan Nuwamba, domin baiwa daliban da ke zana jarabawar kammala sakandire damar zana jarabawar."

A yayin da yake sanar da rike sakamakon jarabawar daliban da suka zana a cikin cibiyoyin gyara hali, ya ce, "Akwai daliban da suka zana jarabawa a cibiyoyin gyara hali da ke fadin kasar.

"Sai dai mun gano cewa akwai daliban da sam ba 'yan bursina bane; mun aikawa cibiyoyin wasika, su sanar damu yadda akayi hakan ta faru.

"Saboda bamu son wani wanda ba bursuna ba ya zo ya samu garabasar da muka baiwa bursunoni."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel