Da duminsa: FG ta umurci ma'aikata da ke a mataki na 12 da 13 su koma bakin aiki
- An umurci ma'aikata da ke a matakin 12 da 13 da kuma wadanda ke muhimmin aiki da su koma bakin aiki
- Umurnin ya fito ne a cikin wata sanarwa daga shugaban ma'aikata na gwamnatin tarayya, Dr Folashade Yemi-Esan
- Duk ma'aikatan da zasu dawo bakin aiki zasu rinka aikin ne daga ranar Litinin zuwa Juma'a, daga misalin karfe 8 na safe zuwa karfe 4 na yamma
Gwamnatin tarayya ta umurci ma'aikatan da ke a matakin 12 da 13 da kuma wadanda ayyukansu na musamman ne da su koma bakin aikinsu.
Umurnin ya fito ne daga cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban ma'aikata na gwamnatin tarayya, Dr Folashade Yemi-Esam, a ranar Litinin, 10 ga watan Agusta.
Kafin wannan, ma'aikata a mataki 14 da sama ne kawai suka koma aiki, inda suke aiki na tsawon kwanaki uku kacal, saboda annobar COVID-19.
KARANTA WANNAN: Buhari ya shiga ganawa da gwamnonin Arewa maso Gabas da hafsoshin tsaro

Asali: Facebook
Amma da wannan sabon umurnin, dukkanin ma'aikatan da zasu dawo bakin aiki zasu rinka zuwa ne daga ranar Litinin zuwa Juma'a, daga karfe 8 na safe zuwa karfe 4 na yamma.
Kadan daga cikin sanarwar na ce: "Biyo bayan amincewar shugaban kasa kan bukatar kwamitin PTF, an umurci ma'aikata a matakin 12 da 13 su koma bakin aiki.
"Za su rinka zuwa aiki daga ranar Litinin zuwa Juma'a, kuma zasu fara ne daga ranar Litinin, 10 ga watan Agusta, 2020.
"Haka zalika, ma'aikatan da abun ya shafa, zasu rinka zuwa aikin ne daga karfe 8 na safe zuwa 4 na yamma a kowacce ranar aiki."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng