Yanzu-yanzu: Direbobin tankar man fetur sun shiga yajin aiki

Yanzu-yanzu: Direbobin tankar man fetur sun shiga yajin aiki

Daga ranar Litinin 10 ga watan Augusta, kungiyar matuka motocin daukar man fetur ta jihar Lagos za ta shiga yajin aiki bisa umurnin kungiyar ma'aikatan man fetur da iskar gasar ta kasa NUPENG.

Shugaban kungiyar NUPENG, Tayo Aboyeji, ya tabbatar da hakan a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Litinin a birnin Lagos.

Mr Aboyeji ya ce yajin aikin zai fara da safiyar ranar 10 ga watan Agusta, biyo bayan gaza cimma wata yarjejeniya tsakanin kungiyar da gwamnati.

"Duk da cewa, mun hadu da gwamnatin jihar a daren jiya (9 ga watan Agusta), amma bamu cimma matsaya ba.

"Don haka, direbobin tanka na jihar Lagos ne kawai zasu shiga yajin aikin, saboda rashin kyakkyawan muhalli na aikinmu," a cewarsa.

KARANTA WANNAN: Zawarcin shiga APC: Gwamna Ortom ya ce ba zai bar jam'iyyar PDP yanzu ba

Yanzu-yanzu: Direbobin tankar man fetur sun shiga yajin aiki
Yanzu-yanzu: Direbobin tankar man fetur sun shiga yajin aiki
Asali: Facebook

NAN ta ruwaito cewa kungiyar NUPENG a ranar 7 ga watan Agusta ta umurci mambobinta da su shirya shiga yajin aiki daga ranar 10 ga watan Agusta.

Shugaban NUPENG na kasa, Williams Akporeha, da sakataren kungiyar Olawale Afolabi a cikin wata sanarwa sun bayyana cewa yajin aikin ya zama dole saboda nuna halin ko in kula da ake yi ga bukatun da suka mikawa gwamnatin.

Bukatun sun hada da daina karba kudade a hannun direbobi da jami'an tsaro ke yi a tituna; ajiye kwantenoni ba bisa ka'ida ba a titunan Apapa, Kirikiri da Beach Land dake jihar.

Sauran sun hada da cin zarafi da barazana da mambobinsu ke fuskanta daga 'yan iskan unguwa da kuma uwayen gidansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel