Zawarcin shiga APC: Gwamna Ortom ya ce ba zai bar jam'iyyar PDP yanzu ba

Zawarcin shiga APC: Gwamna Ortom ya ce ba zai bar jam'iyyar PDP yanzu ba

- Gwamna Samuel Ortom ya ce ba shi da wani burin barin jam'iyyar PDP a yanzu

- Gwamnan ya bayyana cewa ya samu tayi na shiga jam'iyya mai mulki ta APC

- Ortom ya sha alwashin yin aiki tukuru don ganin jam'iyyar PDP ta samu nasara a zaben 2023

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya ce a halin yanzu ba shi da wani buri na barin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), domin komawa tsohuwar jam'iyyarsa ta APC.

Gwamna Ortom ya bayyana hakan a taron APC na zabar kwamitin shugabanci na jam'iyyar a jihar, inda mulki ya ci gaba da zama a hannun John Ngbede.

A taron, Ortom ya ce jam'iyyar APC ta kawo mashi goron gayyatar shiga jam'iyyar, amma bai karba ba, ya ce zai ci gaba da zama a jam'iyyar PDP.

Haka zalika, wakilan zaben sun nuna gamsuwarsu da shi na kin komawa APC, bayan da wakilan suka nuna mashi rashin alfanun barin jam'iyyar PDP.

KARANTA WANNAN: COVID-19: Yan Nigeria 311 sun dawo daga UAE, sun sauka Abuja

Zawarcin shiga APC: Gwamna Ortom ya ce ba zai bar jam'iyyar PDP yanzu ba
Zawarcin shiga APC: Gwamna Ortom ya ce ba zai bar jam'iyyar PDP yanzu ba
Asali: UGC

A yanzu da aka warware wannan, an kawo karshen sabanin da ake samu na kama kamar shugabanci a jihar, inda ake zargin kabilar Tiv ce ke mulki tun 1976.

A yanzu, sanatan da ke wakiltar Benue ta Kudu, Abba Moro da tsohon shugaban majalisar dattinai, David Mark, sun tabbatar da cewa shiyyar za ta kawo gwamna a zaben 2023.

Bayan samun yabo daga jama'a da komawarsa kujerarsa, wakilan zabe suka ci gaba da kad'a kuri'arsu ga 'yan takarar kujeru 39, bisa jagorancin Mr. John Ngbede.

Wasu daga cikin jigogin 'yan siyasa da suka halarci taron na ranar Asabar sun hada da tsohon shugaban majalisar dattijai, David Mark da Iyorchia Ayu, da kuma sanatoci masu wakiltar Benue a majalisar dattijai ta kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel