'Yan bindiga sun bi hadimin gwamna a harkar tsaro har gida sun kashe

'Yan bindiga sun bi hadimin gwamna a harkar tsaro har gida sun kashe

- A ranar Lahadi da sa'o'in farko, wasu da ake zargin bata gari ne sun kutsa gidan hadimin Gwamna Obiano inda suka soka masa wuka

- Wani ganau ba jiyau ba ya ce, Azubuike Ekwegbalu, babban mataimakin na musamman a kan tsaro ya rasu ne sakamakon soka masa wukar da aka yi

- Jam'ian tsaro sun gaggauta zuwa wurin da al'amarin ya faru inda suka mika shi asibiti sannan likitoci suka tabbatar da mutuwarsa

Wasu miyagu a ranar Lahadi sun tsinkayi gidan Azubuike Ekwegbalu, babban mataimaki na musamman ga Gwamna Willie Obiano a kan tsaro, inda suka kashe shi ta hanyar soka masa wuka.

An gano cewa, lamarin ya faru ne a sa'o'in farko na ranar Lahadi a gidansa da ke kwatas na kwamishinoni a Awka, yankin da manyan jami'an gwamnati suke.

Wani ganau ba jiyau ba yace, marigayin dan asalin Ogbunike da ke karamar hukumar Oyi ta jihar, dan uwan matar gwamnan ne.

"Wasu mutane ne suka kashesa a daren jiya. Wannan zalumci ne. Ubangiji ya gafarta masa.

"Dole ne jami'an tsaro su yi iyakar kokarinsu wurin tsamo wadanda suka yi kisan," majiyar tace.

Kakakin Rundunar 'yan sandan jihar, SP Haruna Mohammed, ya ce an damke wani mutum daya da ake zargi a farfajiyar wurin.

'Yan bindiga sun bi hadimin gwamna a harkar tsaro har gida sun kashe
'Yan bindiga sun bi hadimin gwamna a harkar tsaro har gida sun kashe. Hoto daga The Nation
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Bukatu 4 da gwamonin arewa maso gabas suka mika ga FG

"A ranar 9 ga watan Augustan 2020 wurin karfe 1:30 na safe, an samu rahoton kisan wani Azubuike Ekwegbalu mai shekaru 43 dan asalin Ogbunike da ke karamar hukumar Oyi, mazaunin kwatas din kwamishinoni.

"Bayan rahoton, jami'an 'yan sanda da suka samu jagorancin CSP Emma Ogbuanya, sun ziyarci wurin tare da gaggauta mika shi asibitin COOUTH da ke Awka.

"A nan aka tabbatar da mutuwarsa. Gawarsa na ma'adanar gawawwaki da ke asibitin don bincike a kan abinda ya kashe sa," yace.

Mohammed ya ce, duba na tsanaki ga gawarsa na nuna cewa sukarsa aka yi da wuka kuma an ga wuka a inda lamarin ya faru.

"Amma kuma, wani mutum daya da ake zargi ya shiga hannun jami'an tsaro kuma ana bincikarsa don gano bakin zaren," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel