Yadda za a kawo karshen tawaye: Tattaunawa da wani ɗan Boko Haram da ya tuba

Yadda za a kawo karshen tawaye: Tattaunawa da wani ɗan Boko Haram da ya tuba

Manema labarai na jaridar Daily Trust sun tattauna da wani tsohon dan kungiyar masu tayar ta Boko Haram da ya tuba, Abdulwahab Usman.

Abdulwahab dai matashi ne mai shekaru 32 a duniya wanda kuma ya fito daga karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

Matashin yana daya daga cikin tubabbun ‘yan Boko Haram da a baya bayan nan aka yaye daga makarantar zare akidar ta’adddanci da gyara hali karkashin gudanarwa dakarun tsaro ta Operation Safe Corridor.

Yayin tattaunawa da manema labarai, Abdulwahab ya bayyana yadda za a kawo karshen tawayen kungiyar Boko Haram da ya-ki-ci-ya-ki-cinyewa tsawon shekaru fiye da goma da suka shude.

Tambaya: Ta ya ka shiga kungiyar Boko Haram?

Amsa: Na shiga kungiyar Boko Haram ne a shekarar 2014 a lokacin da nake tsare a Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

A wannan lokaci sai ‘Yan Boko Haram suka kawo hari Barikin domin kubutar da mambobinsu da ke tsare.

Mu da aka tsare saboda wasu laifukan na daban, ‘yan tawayen suka tattara suka kai mu wani daji inda a nan muka karbi akidarsu. A haka na shiga kungiyar kuma na shafe shekaru 7 a cikinsu.

Tambaya: Wane laifi ka aikata da ya sa aka tsare ka a Barikin Giwa inda ‘yan tawayen suka kubutar har da kai?

Wasu abokonai na tun muna yara da muka yi makarantar sakandire tare, sune suka rinjaye ni wajen shiga kungiyar.

Sunayensu na daga cikin mambobin Boko Haram da dakarun tsaro k enema ruwa a jallo, kuma saboda alakar da ke tsakani na da su ta sanya a kama ni tare da kuma a ka tsare mu a barikin.

Tambaya: Menene matsayinka a kungiyar kuma wane aiki ne ya rataya a wuyanka?

Amsa: Ina daga cikin wadanda ake turawa kai hare-hare garuruwa, amma ban taba yunkurin yin kunar bakin wake ba koda sau daya.

Tambaya: Daga cikin hare-haren da ka kai, wane yafi b aka wahala kuma ba z aka iya mantawa da shi ba?

Amsa: Akwai wani hari da muka kai wa sojoji a kauyen Konduga na jihar Borno. Daga cikin mu 74 da muka kai harin, 34 sun rasa rayukansu, sai mu 40 da muka sha da kyar.

A kan hanyar mu ta dawo wa kuma, sai ga jirgi mai saukar Ungulu yana sintirin neman mu kuma mun tabbatar cewa zai yi mana wahala mu tsira, hakan ya sanya muka mika wuya.

KARANTA KUMA: Ganduje ya kudiri aniyyar tallafawa malaman makarantu masu zaman kansu a Kano

Tambaya: A matsayin na tsohon dan tawaye wanda kuma ya tuba, me kake ganin ya dace gwamnati ta yi domin kawo karshen wannan lamari cikin gaggawa?

Amsa: Gwamnati ta bada tabbacin cewa babu abin da zai samu duk dan tawayen da ya tuba kuma ya mika wuya. Ina da tabbacin cewa duk za su saduda.

Tambaya: A lokacin da kake cikin mayakan Boko Haram, mutum nawa ka kasha?

Ba zan iya tuna ainihin adadin ba, amma na kashe mutane da dama.

Tambaya: Wane sako gare ka zuwa ‘yan tawayen da ke ci gaba da fafata wa sojoji a dokar daji?

Amsa: Ina kira da su sadudu kuma su mika wuya ga dakarun sojin Najeriya. Za a zare musu akidar ta’addanci da gyara halayyarsu kuma a maida su cikin al’umma su ci gaba da rayuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel