A cikin sabon bidiyo, Shekau ya yi wa Shettima, Zulum, Monguno, Bukarti da Dalung barazana

A cikin sabon bidiyo, Shekau ya yi wa Shettima, Zulum, Monguno, Bukarti da Dalung barazana

Shugaban kungiyar masu tayar da kaya ta Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki sabon bidiyo wanda ke barazana ga tsoho da kuma gwamnan jihar Borno na yanzu, Kashim Shettima da Babagana Zulum.

Haka kuma Shekau ya ja kunne mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Babagana Monguno da manazarci kan kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi, Bulama Bukarti da tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung.

A cikin faifan bidiyon na tsawon mintuna 56, Shekau ya fassara taken Najeriya da taken Hukumar bautar kasa ta NYSC zuwa harshen Larabci, Hausa da kuma Kanuri.

Ya yi ikirarin cewa duk musulman Najeriya da suke karanta taken, to ba masu Imani bane kuma sun cancanci a kashe su.

Abubakar Shekau
Abubakar Shekau
Asali: Facebook

Ya tafi a kan cewa, duk Musulmin da ya karanta taken Najeriya a makaranta ko a wani wurin na daban, to kafiri ne ko da kuwa yana Sallah ya na Azumi.

A rukunin harshen Kanuri na bidiyon kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, Shekau ya yi wa mutanen barazana wanda kusan dukkaninsu sun kasance ‘yan kabilar Kanuri.

Ya kiraye su da sunayensu daya-bayan-daya, tare da gargadin cewa duk wanda ya karanta taken Najeriya “ko da kuwa da wasa, to ya zama kafiri walau yana Sallah da azumi.”

Wannan sabon bidiyo ya fito ne a yayin da a baya bayan nan kasar Amurka ta yi gargadin cewa, kungiyar Boko Haram ta fara fadada shinge daga yankin Arewa maso Gabas zuwa Arewa maso Yamma.

A wani bidiyon da shugaban ‘Yan ta’addan kungiyar Boko Haram ya fitar kwanan nan, an ji ya na gargadin Bulama Bukarti tare da wasu shugabannin gwamnati da Sojojin Najeriya.

KARANTA KUMA: Buhari ya yaba wa Tambuwal da Sultan kan tsaro a Sakkwato

Abubakar Shekau ya kuma ja kunnen Ministan sadarwa na Najeriya, Isa Ali Ibrahim Pantami da shugaban kasa Muhammadu Buhari da Shugaban hafsun Soji, Janar TY Buratai.

Bulama Bukarti wanda Masanin shari’a ne kuma Mai karatun Digirinsa na uku watau PhD a Jami’ar SOAS ta Ingila, ya fito ya maida martani bayan jawabin Abubakar Shekau.

Audu Bulami Bukarti ya nuna cewa ya san dalilin da ya sa ya zama kayar-bayan ‘Yan kungiyar ta’addan Boko Haram. Audu Bukarti ya yi wannan jawabi ne a shafinsa na Tuwita.

A cewar Malam Bulama Bukarti wanda bincikensa daga cibiyar Tony Blair ta Duniya su ka zagaye ko ina, ‘Yan Boko Haram su na kokarin toshe bakinsa ne, wanda ba zai yiwu ba.

Duk da wannan barazana, Bulama Bukarti ya bayyana cewa ba za a taba tursasa masa ya yi gum ba, hakan ya na nufin zai ci gaba da magana a kan ‘Yan ta’addan na Boko Haram.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel