Bukatu 4 da gwamonin arewa maso gabas suka mika ga FG

Bukatu 4 da gwamonin arewa maso gabas suka mika ga FG

Kungiyar gwamnonin arewa maso gabas sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tura 'yan sanda don yakar Boko Haram a yankin, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Kungiyar ta sanar da hakan ne a wata takarda da ta fitar bayan taronta karo na biyu da tayi don tattaunawa a kan kalubalen da yankin ke fuskanta.

Takardar ta samu saka hannun shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum.

Ta jinjinawa kokarin gwamnatin tarayya wurin yaki da ta'addancin, amma tayi kira ga dakarun soji da su tsananta tsaro wurin tabbatar da cewa manoma a yankin za su iya komawa gonakinsu.

"Kungiyar ta bukaci cewa , a rufe gibin rashin ma'aikata isassu ta hanyar tura jami'an 'yan sanda don tsaro sannan a samar musu da kayayyakin aiki isassu," takardar tace.

Ta yi kira ga ma'aikatar ruwa ta tarayya da ta mayar da hankali wurin cike tafkin Chadi tare da karfafa sauran rafukan da ke yankin.

Takardar ta ce, gwamnonin shida sun dauka alwashin aiki tare don tabbatar da hadin kai, ci gaba da habakar yankin ballantana a fannin hako man fetur, noma da kuma masana'antu.

Takardar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kwace ayyukan tituna da ma'aikatar ayyuka ta bada na tsawon shekaru ba tare da an yi ba sannan ta bai wa 'yan kwangilar da suka shirya yi.

Bukatu 4 da gwamonin arewa maso gabas suka mika ga FG
Bukatu 4 da gwamonin arewa maso gabas suka mika ga FG. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mai Deribe: Mamallakin fadar zinari a Najeriya da ke saukar manyan shugabannin duniya

Takardar ta kara da kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da cewa an ci gaba da aikin janyo wuta na Mambila da sauran ayyukan ci gaba da hukumar kula da habaka yankin arewa maso gabas ke yi.

"Kungiyar na sake jaddada goyon bayanta ga gwamnatin tarayya ta yadda ta mayar da hankali wurin gyara tsarin almajiranci tare da karfafa ilimin addini da na Boko, hana bara a tituna da kuma mayar da yara kanana makaranta.

"Kungiyar ta nada Zulum a matsayin shugabanta na tsawon shekaru biyu kuma za a kafa babban ofishin kungiyar a Maiduguri," takardar tace.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, taron ya samu halartar gwamnonin jihar Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel