Buhari ya yaba wa Tambuwal da Sultan kan tsaro a Sakkwato

Buhari ya yaba wa Tambuwal da Sultan kan tsaro a Sakkwato

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba wa gwamnatin jihar Sakkwato da kuma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, dangane da sa ido kan sha’anin inganta tsaro.

Gwamnatin tarayya ta yi wannan yabo ga Sultan da kuma gwamnatin Sakkwato karkashin jagorancin gwamna Aminu Waziri Tambuwal a sakamakon hadin kan da suka bata a kokarin da take yi na kawo karshen rashin tsaro a kasar.

Buhari ya yi wannan yabo a ranar Asabar yayin da ya halarci daurin auren ‘yar Sarkin Musulmi, Zainab Fodio da aka gudanar a fadar Sarkin da ke birnin Shehu.

Jaridar ThePunch ta ruwaito cewa, Ministan Shari’a kuma Lauyan koli na kasa, Abubakar Malami, shi ne ya jagoranci tawagar da ta wakilci shugaban kasa Buhari a taron na daurin aure.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Sauran ‘yan tawagar sun hadar da Ministan kula da Harkokin ‘Yan Sanda, Muhammad Maigari Dingyadi da kuma Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Muhammad Adamu.

Shugaban kasar ya ce Gwamna Tambuwal da Sultan sun jajirce a kan yaki da ta’addancin masu tayar da kayar baya kamar ‘yan daban daji da sauran masu tayar da zaune tsaye.

Babu shakka a baya bayan matsalar rashin tsaro ta ci gaba da tsananta a fadin kasar musamman yankunan Arewa maso Gabas da kuma Arewa maso Yamma.

A dalilin hake na ya sanya shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya nemi shugaban kasa Buhari da ya yi murabus ganin yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a kasar.

KARANTA KUMA: An bani goron gayyatar koma wa APC - Ortom

Tun a waran Janairu ne dai Sanata Abaribe ya yi wannan kira yayin wata tattauna a wani zaman majalisar dattawa kan kudirin da aka gabatar na kalubalen tsaro da ya addabi kasar.

Yayin zaman, Abaribe wanda shi ne ya fara tofa albarkacin bakinsa, ya soki shugaba Buhari da cewa ya gaza magance matsalar tsaro wadda kuma shi ne nauyi na farko da kundin tsarin mulkin kasa ya rataya a wuyansa.

Sanatan ya fusata kan yadda shi kanshi shugaban kasar yake ikirarin mamakin yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa alhali shi yake rike da akalar jagoranci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel